2027: Makomar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na janyo cece-kuce
Published: 7th, June 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya samu goyon bayan manyan jiga-jigan jam’iyyar APC domin sake tsayawa takara a zaɓen 2027, amma sunan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima bai fito ba yayin tattaunawar lamarin da ya haifar da tambayoyi game da makomarsa a siyasa.
Ko da yake Shettima ya halarci babban taron jam’iyyar APC na ƙasa, inda aka nuna wa Tinubu goyon baya, amma ba a ambaci sunansa ba a wajen taron.
Wannan ya sa mutane da dama suka fara tunanin ko zai dawo a matsayin mataimaki ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027.
Wasu ’ya’yan jam’iyyar na cewa, goyon bayan Tinubu ba yana nufin goyon bayan Shettima ba.
“Zaɓi ne da ke hannun shugaban ƙasa wanda zai zaɓa mataimakinsa,” in ji Cif Sam Nkire, ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC.
“Mataimakin shugaban ƙasa dole ya ci gaba da zama lafiya da mutane domin shugaba ya ci gaba da amincewa da su.”
Akwai damuwa daga ɓangaren Arewa maso Gabas, yankin Shettima, inda wasu ke buƙatar a fito a bayyana matsayin mataimakin shugaban ƙasa kafin lokacin zaɓen.
“Muna buƙatar bayani,” in ji Barrista Abdullahi Jalo.
“Shiru a kan Shettima ba abu ne da za a wuce haka kawai ba, kuma ya cancanci a yi wa yankin bayani.”
Har yanzu dai Jihar Borno ce kaɗai daga Arewa maso Gabas da ta fito fili ta nuna goyon bayan Tinubu da Shettima tare.
Masana siyasa suna cewa tarihin Tinubu na canja mataimaka a lokacin da yake gwamnan Legas, inda ya sauya mataimakin gwamna sau uku na iya sake maimaituwa a matakin ƙasa.
Daraktan Yaɗa Labaran APC, Bala Ibrahim, ya jaddada cewa goyon bayan da aka nuna wa Tinubu ya shafi ofishin shugaban ƙasa gaba ɗaya.
“Idan jam’iyya na goyon bayan shugaban ƙasa, to ba a cire mataimakinsa daga ciki ba, sai dai idan shi ya bayyana hakan da kansa.”
Sai dai rashin hoto ko sunan Shettima a cikin tallace-tallacen kamfen ɗin Tinubu da bayanan jam’iyya yana ƙara jefa shakku a zukatan wasu.
Mutane da dama a Arewa maso Gabas na jin kamar ana ƙoƙarin watsar da su, musamman ganin yadda Arewa maso Yamma ke ci gaba da riƙe manyan muƙamai a gwamnatin yanzu.
Ana sa ran za a gudanar da wani babban taro na APC a Gombe a ranar 16 ga watan Yuni don duba wannan lamari.
Masu ruwa da tsaki za su tattauna kan tikitin 2027 da kuma yiwuwar tabbatar da tikitin Tinubu da Shettima.
Amma har yanzu, tambayoyi kan makomar Shettima ba su samu amsa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: abokin takara Goyon Baya Siyasa Zaɓen 2027 goyon bayan
এছাড়াও পড়ুন:
Trump ya fitar da Amurka daga UNESCO saboda amincewa da Falasdinu a matsayin Mamba
Amurka ta yanke shawarar ficewa daga hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a karo na biyu saboda matakin da ta dauka na shigar da Falasdinu a matsayin mamba.
Mataimakiyar sakatariyar yada labaran fadar White House Anna Kelly ta sanar da matakin a cikin wata sanarwa a ranar Talata.
Kelly ta ce dalilin da ya suka dauki wannan kan hukumar UNESCO, shi ne ta tallafa wa shirye-shiryen da Amurka ke kallonsu a matsayin wadanda ba su dace da muradunta ba.
“Shugaba Trump ya yanke shawarar janye Amurka daga UNESCO, wadda ke kula da ayyuka a bangaren raya al’adu da ilimi da zamantakewar al’umma, saboda daukar wau matakai wadanda ba su dace da manufofin Amurka ba,” in ji Kelly.
Ta ci gaba da cewa, shigar da Falasdinu a matsayin mamba a hukumar UNESCO, Amurka na Kallon hakan a matsayin babbar matsala kuma ya saba wa manufofin Amurka, wanda hakan ke ke kara haifar da karuwar kalaman kyama ga Isra’ila a cikin kungiyar.
Darakta-janar na UNESCO, Audrey Azoulay, ya bayyana matukar Rashin jin dadinsa kan matakin da Trump ya dauka na ficewa daga kungiyar, amma ya kara da cewa dama tuni aka yi hasashen haka, kuma UNESCO ta shirya ma hakan, tare da yin nuni da cewa hukumar ta dauki matakin karkata hanyoyin samar da kudadenta, inda kusan kashi 8% na kasafin kudin ta ke fiowa daga Washington.