Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Ta’adda, Sun Kashe Wasu Da Yawa A Borno
Published: 5th, June 2025 GMT
A wani cigaba makamancin haka, dakarun Mallam Fatori suma sun daƙile wani yunƙurin hari daga ‘yan ta’adda da suka zo ta wurare daban-daban.
Ya ce bayan sa’o’i na musayar wuta, dakarun sun bi ‘yan ta’addan da suka tsere, inda suka hallaka da dama, wasu kuma suka gudu da raunukan harbin bindiga. An kuma kwato muggan makamai da dama kamar bindigogi AK-47, da bindigar kakkaɓo jirgi (RPG), da sauran kayayyakin yaƙi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun Amurka ta daure ’yan Najeriya 5 shekaru 159 kan aikata damfara
Wata kotu a kasar Amurka ta yanke wa wasu ’yan Najeriya su biyar hukuncin daurin shekaru 159 bisa samun su da da laifin damfarar Amurkawa sama da 100.
Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin damfarar kamfanoni da hukumomin gwamnatin kasar kudin da yawansu ya kai Dala miliyan 17, kwatwankwacin Naira biliyan 27 da miliyan 200.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sashen shari’a na kasar ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Laraba, mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin Babban Lauyan gwamnati na gundumar gabashin Texas, Ray Combs.
’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina Yadda manoma suka yi addu’ar roƙon ruwa a ZamfaraSanarwar ta ce mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da Damilola Kumapayi, Sandra Iribhogbe, Edgal Iribhogbe, Chidindu Okeke and Chiagoziem Okeke, kuma mambobi ne a wani gungun ’yan damfara na kasa da kasa.
Lauyan ya ce ’yan damfarar sun fara harkallar ne tun a shekara ta 2017, inda suke hakon tsofaffi da kuma masu rangwamen gata ta hanyar kirkiro dabaru daban-daban na karbar kudi daga wajensu, wasu lokutan ma ilahirin abin da suka tara a rayuwarsu.
“Da zarar sun karbi kudade daga mutane ta hanyar damfarar, sai su tuttura su ta hanyar asusun ajiya a bankuna da dama da kuma abokan harkallarsu da ’yan kasuwa da ke kasashe a nahiyoyin Afirka da Asiya,” in ji lauyan na gwamnatin Amurka.
Sanarwar ta ce bayan kama su, an gurfaran da su a gaban kotu kan laifukan da suka hada da hadin baki, zambar kudade da kuma damfara, wadanda dukkansu suka amsa aikatawa.
A cewar sanarwar, hakan ce ta sa alkalin kotun, Mai Shari’a Amos Mazzant, ya yanke musu hukuncin daurin shekaru daban-daban a kurkuku.