Ɓarawon waya ya kashe babban jami’in soja da wuƙa a Kaduna
Published: 9th, June 2025 GMT
Wani babban jami’in soja, Laftanar Commodore M. Buba, ya rasa ransa bayan da wani ɓarawon waya ya soka masa wuƙa a ƙirji.
Lamarin ya faru ne a gadar Kawo, lokacin da jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar Horas da Sojoji ta Armed Forces Command and Staff College (AFCSC).
Shaidu sun bayyana cewa yayin da jami’in ke cikin gyara tayar, sai wani mutum ya zo ya buƙaci ya ba shi wayarsa.
Jami’in soja ya ƙi bayar da wayar, inda ɓarawon ya ciro suka ya soka masa a ƙirji.
Wani jami’in sa-kai, Suleiman Dahiru, wanda ya ga abin da ya faru, ya yi ƙoƙarin taimaka masa, amma shi ma ɓarawon ya yanke shi da wuƙa a hannu.
Mutanen da ke kusa da wajen take suka kashe ɓarawon da duka.
An garzaya da jami’in sojan zuwa Asibitin Manaal, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Daga baya an ɗauki gawarsa zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin 44 Nigerian Army Reference Hospital da ke Kaduna.
Wani babban jami’in soja da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun shiga cikin gari cikin kaya domin gudanar da bincike da kuma kawar da masu aikata laifuka a Kaduna.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar ƙoƙarin ƙara tsaurara matakan tsaro a faɗin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kawo
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso.
Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa.
A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka daga jami’an lafiya.
Sai dai ’yan Najeriya da dama sun dade suna kokawa da yadda a cewarsu wasu jami’an kiwon lafiya kan nuna halin ko-in-kula, a wasu lokutan ma da sakaci, wanda kan kai rasa rayuka.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai zube komai a faifai don gano sahihancin wannan zargi da ’yan Najeriya suke yi da kuma, idan zargin ya tabbata, yadda aikin jami’an lafiya ya yi hannun riga da abin da aka karantar da su.
Domin sauke shirin, latsa nan