Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 7 a Sakkwato
Published: 4th, June 2025 GMT
Wasu mutum bakwai sun rasa ransu sakamakon hatsarin kwale-kwale lokacin da suke tafiya daga kauyen Gidan Husaini zuwa Gwargawu na karamar hukumar Shagari a jihar Sakkwato ranar Litinin.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da mamatan ke tafiya a wani kogi, lamarin da ya jefa mutanen yankin cikin jimami da alhini.
Ba a dai bayyana sunayen wadanda suka rasun ba, amma hukumomi a yankin sun tabbatar da cewa dukkan mamatan ’yan asalin kauyen na Gidan Husaini ne.
Ambaliyar Mokwa: Yawan mutanen da suka salwanta ya haura 700 Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin gwauron zaboDa ya jagoranci wata tawagar gwamnatin jihar domin yin ta’aziyyar mamatan, Kwamishinan Kudi na jihar, Muhammadu Jabbi Shagari, ya bayyana hatsarin a matsayin rashi ga ilahirin mazauna yankin, jihar da ma al’ummar Musulmi baki daya.
Sai dai Kwamishinan ya yi kakkausan gargadi ga matuka kwale-kwalen a kan yin lodin da ya wuce kima, inda ya ce rayuwar mutane ta fi komai za a samu muhimmanci.
Sai dai hatsarin ya sake fito da damuwar da ake da ita kan harkar sufuri ta ruwa a yankunan karkarar jihar, inda mutane suka dogara da kwale-kwalen saboda karancin jiragen ruwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin kwalekwale Sakkwato kwale kwale
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar
Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen inganta ci gaban zamantakewar al’umma da kuma tallafawa aiwatar da Muradun Cigaba mai Dorewa (SDGs).
Hajiya Amina Mohammed ta kai ziyara Jihar Kano ne domin yin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar fitattun dattawan nan biyu, wato Alhaji Aminu Alhassan Dantata da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
A yayin ziyarar tata, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna gamsuwa da wasu daga cikin shirye-shiryen Gwamna Yusuf na cigaban al’umma, musamman wadanda suka yi daidai da muradun ci gaban duniya.
Daga cikin wadannan shirye-shirye akwai sanya fitilu masu amfani da hasken rana a titunan Kano, kafa cibiyar kula da cututtuka ta Kano (Kano Centre for Disease Control), wadda ita ce irinta ta farko da wata gwamnati ta jiha ta kafa a Najeriya, da kuma kokarin fadada tsarin inshorar lafiya domin al’ummar jihar su amfana.
Ta kuma yaba da kirkirar Ma’aikatar Wutar Lantarki da Makamashi, tare da sake tsara Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, wanda dukkansu ke nuni da jajircewar gwamnati wajen daukar matakan kare muhalli da dorewar ci gaba.
Hajiya Mohammed ta bayyana cewa ziyarar tata ba wai kawai domin ta’aziyya ba ce, har da zurfafa wayar da kai kan Muradun Ci Gaba Mai Dorewa, da kuma karfafa hadin gwiwa da jihar Kano.
Ta sanar da gwamnan game da babban taron Kasuwanci da Zuba Jari na Majalisar Dinkin Duniya da ke tafe, tare da nuna godiya bisa dagewarsa wajen karfafa mata, samar da ayyukan yi, da kare muhalli.
A nasa jawabin , Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa a shirye jiharsa take ta hada gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya musamman a fannonin ilimi, lafiya, sauyin yanayi, samar da makamashi, kare muhalli da kuma zuba jari mai dorewa.
Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaba da za su inganta rayuwar al’ummar Kano da kuma bada gudunmawa ga kokarin ci gaban duniya.
Abdullahi Jalaluddeen