Ambaliyar Mokwa: An gano gawar yara 7, jama’a na neman agaji
Published: 4th, June 2025 GMT
An gano gawar yara bakwai a yankin Mokwa, da ke Jihar Neja, bayan ambaliyar ruwa da ta afka wa garin mako guda da ya wuce.
Yawan adadin waɗanda suka rasu kawo yanzu ya kai mutum 160, amma wasu jami’ai sun ce za a iya gano gawar sama da mutum 200.
Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano Sallah: Mun shirya samar da tsaro a Yobe — ’Yan SandaAmbaliyar ta kuma tafi da motar haya mai kujeru 18 ɗauke da fasinjoji.
Kawo yanzu, bayan kwana shida da faruwar ambaliyar, ba a ga motar ko wani daga cikin fasinjojin ba.
Wani mazaunin garin, Baba Abu, ya ce: “Direban bai nemi ƙetare ruwan ba. Ya tsaya gefe yana jira ruwa ya ragu.
“Amma sai ruwan ya ƙaru ya kwashe motar ya jefa ta cikin Kogin Neja. Har yanzu ba mu san inda ta ke ba.”
Wasu daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa sun koka cewa ba sa samun kayan tallafi, duk da cewa gwamnati ta ce tana rabawa.
Hadiza Saidu, wadda ta rasa mahaifiyarta da komai nata, ta ce: “Da kayan jikina guda ɗaha da hijabi na tsira da su. Idan muka je karɓar tallafi, sai a ce ya ƙare. Wasu da ambaliyar ba ta shafa ba ake bai wa tallafin.”
Mutane sun fusata bayan wasu manyan cirarun jami’an gwamnati ne kawai suka ziyarci Minna, ba tare da sun je Mokwa inda ambaliyar ta faru ba.
Ƙungiyoyi da mazauna yankin sun ce hakan bai nuna an tausaya waɗanda lamarin ya shafa ba.
Gwamnati ta ce ambaliyar ta samo asali ne daga ruwan sama mai ƙarfi da kuma lalatacciyar hanyar ruwa, ba daga buɗe dam ba.
Masana da Ƙungiyar Tsofaffin Arewa (NEF), sun buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa da kuma kare sake faruwar hakan a gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa gwamnati Mokwa da ambaliyar ambaliyar ta
এছাড়াও পড়ুন:
NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe, sun fara rabon kayayyakin gini ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Wannan taimako na da nufin tallafa wa mutanen da ambaliya ta rushe musu gidaje.
Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido An kone babur din ‘barayin waya’ a KanoA lokacin da aka fara rabon kayayyakin a Damaturu, wakilin babban daraktan NEDC, Farfesa Ibrahim Ali Abbas, ya ce hukumar ta kawo kayayyakin rufin gida da sauran kayan gini don taimaka wa mutane su gyara ko sake gina gidajensu.
Baya ga wannan, hukumar ta kuma bai wa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), kayan aikin ceto, domin su kasance cikin shiri idan wani iftila’i ya sake faruwa a wannan daminar.
Babban jami’in na NEDC ya roƙi shugabanni da su raba kayan cikin gaskiya da adalci, kuma a tabbatar cewa kayan sun kai hannun masu buƙata yadda ya dace.
A nata ɓangaren, Kwamishiniyar Ma’aikatar Agaji da Jin-ƙai ta Jihar Yobe, Dokta Mairo Ahmed Amshi, ta yaba wa hukumar NEDC saboda taimakon a kan lokaci.
Ta ce wannan matakin zai rage wa mutanen da ambaliya ta shafa raɗaɗi da damuwa.
Ta kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa waɗanda abin ya shafa, da kayan abinci, magunguna da kuma sansanin zama na wucin gadi.
Amma ta buƙaci shugabannin al’umma da su kula da yadda ake raba kayan, sannan ta roƙi wadanda suka samu tallafin da su yi amfani da shi wajen gina gidajen da za su ba su kariya da kwanciyar hankali.