Aminiya:
2025-09-17@23:24:10 GMT

’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano

Published: 4th, June 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sake haramta duk wani nau’i na hawan Sallah a yayin bukukuwan Babbar Sallar da ke tafe.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Talata, ya ce har yanzu haramcin da rundunar ta fitar na nan daram kuma za su tabbatar da an yi aiki da shi a yayin bukukuwan Babbar Sallah ta 2025.

Ya ce sun dauki matakin ne bayan wani zama da ilahirin shugabannin hukumomin tsaro a jihar suka yi, inda ya ce sun gano wani yunkuyi da aka yi wajen yin amfani da hawan wajen yi wa harkokin tsaron jihar zagon kasa, kamar yadda aka samu yayin Karamar Sallar da ta gabata.

Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 7 a Sakkwato Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin gwauron zabo

Sanarwar ta ce, “’Yan sanda suna ba mutane shawara da su bi dukkan dokokin da aka kafa a lokacin bukukuwan.

“Daga cikin dokokin shi ne su kaurace wa hawa doki ko ma kowacce irin dabba da sunan kilisa ko tseren mota ko tukin ganganci ko rike makami.

“Kazalika, an haramta amfani da makami ko kuma duk wani abu da zai iya razanar da jama’a, yayin da ake kiran al’umma da su ja kunnen ’ya’yansu su kauce wa karya doka.

“’Yan sanda da suran jami’an tsaro a shirye suke su tabbatar da an bi wannan doka tare da hukunta wadanda suka karya ta,” in ji sanarwar.

Sai dai umarnin na zuwa ne kasa da kwana biyu bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya umarci Hakimai da su shiga cikin birnin Kano domin fara shirye-shiryen hawan Sallar.

Umarnin wanda ke kunshe a cikin wata wasika da masarautar ta aike wa Hakiman, ta umarce su da su taho tare da dawakai da mahayansu.

Wasikar dai na dauke da sa hannun Sakataren masarautar kuma Dan Makwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf dauke da kwanan watan 30 ga watan Mayun 2025.

Idan za a iya tunawa, ko da Karamar Sallar da ta gabata, Sarkin na Kano ya gudanar da hawan duk kuwa da sanarwar ’yan sandan ta hana shi, lamarin da ya sa hedkwatarsu ta kasa ta gayyace shi, kafin daga bisani ta janye gayyatar bayan abin da ta kira sanya bakin wasu masu fada a ji.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Hawan Sallah

এছাড়াও পড়ুন:

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO
  • KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano