Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin sabbin manyan  sakatarori  guda takwas, da kuma mayar da wasu hudu zuwa wasu ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati daban-daban.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya fitar a Dutse, inda ya bayyana cewa daga cikin sabbin sauye-sauyen akwai Sagir Muhammad Sani daga Ma’aikatar Ilimin Firamare zuwa Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki, da kuma Muhammad Yusha’u daga Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki zuwa Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi.

Sai Lawan Muhammad Haruna daga Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi zuwa Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi, da kuma Injiniya Musa Alhassan Arobade daga Ma’aikatar Wuta da Makamashi zuwa Hukumar Bunƙasa Ma’aikata da Horaswa, wadda ke ƙarƙashin ofishin Shugaban Ma’aikata na Jiha.

Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa, sabbin sakatarorin da aka nada su ne Garba D. Muhammad zuwa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, da Kimiyya da Fasaha, da Fatima Aliyu Hadejia zuwa Hukumar Albashi da Fansho ƙarƙashin ofishin Shugaban Ma’aikata.

Sauran sun haɗa da Baffa Abubakar wanda aka tura zuwa Ma’aikatar Ilimin Firamare, sai Bello Datti zuwa Sashen Kula da Harkokin Musamman/Al’amuran Majalisar Zartarwa ƙarƙashin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, da Ibrahim Hassan zuwa Ma’aikatar Kuɗi, da kuma Nasiru Haruna zuwa Ma’aikatar Wuta da Makamashi, sai Umar Isah zuwa Hukumar Kula da Ma’aikata, yayin da Mahmud Isah Ringim aka tura shi zuwa Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu.

Shugaban Ma’aikatan ya ƙara da cewa, wannan sauyin zai fara aiki ne nan take.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: Taro Tsakanin Iran Da Tawagar Kasashen Turai Dama Ce Ta Gyarar Tunanin Tarai
  • Firaministan Sin Zai Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI 
  • Sojoji Sun Kwato Makamai Daga Hannun Ƴan Bindiga, Sun Ceto Yaro A Filato
  • Binciken CGTN: Masu Bayyana Raayoyi Na Turai Sun Gamsu Da Moriyar Cinikayya Tsakanin Sin Da Turai Sama Da Ta Turai Da Amurka
  • Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC Na Ƙasa, Farfesa Yilwatda
  • Syria: Mutane Da Dama Sun Mutu Da Kuma Jikkata Sanadiyyar Gobara A Rumbun Ajiyar Makamai
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Iran: Sojojin Ruwan Iran Sun Kori Jirigin Yakin Amurka Daga Tekun Oman
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
  • Eritrea ta gargadi Habasha game da yunkurin kafa tashar jiragen ruwa a cikin yankinta