Bangarorin Sudan Da Ke Dauki Ba Dadi Sun Zargi Juna Da Kai Hari Kan Jerin Gwanon Motocin MDD
Published: 8th, June 2025 GMT
Dakarun bangarori biyu na Sudan dake dauki ba dadi, sun zargi juna da kaddamar da hari kan jerin gwanon motocin dake samar da agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya. Motocin dai sun fuskanci barin wuta ne a daren ranar Litinin a Al-Koma na yankin Darfur ta arewa, lamarin da ya sabbaba rasuwar jami’an ayyukan jin kai biyar, tare da jikkatar wasu da dama.
Wata sanarwar hadin gwiwa da shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ko WFP, da asusun UNICEF suka fitar a jiya Talata, ta ce motocin ciki har da manya na dakon kayayyaki 15, suna kan hanyarsu ta zuwa birnin El Fasher mai fama da fari, inda za su kai kayayyakin abinci masu gina jiki lokacin da lamarin ya auku. WFP da UNICEF sun yi Allah wadai da aukuwar wannan lamari, suna musu gargadin cewa hari kan tawagar ma’aikatar jin kai ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Game da aukuwar wannan lamari, ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta zargi rundunar RSF da kaddamar da harin, ta amfani da jirage marasa matuka, tana mai cewa harin ya tarwatsa manyan motocin dakon kaya da dama, da kone wani jirgin aikin ceto, tare da hallaka wasu direbobi, da jami’an tsaro da fararen hula da dama, baya ga wasu da yawa da suka jikkata.
A wata sanarwar ta daban kuma, hukumar samar da agaji da ayyukan jin kai ta Sudan ko SARHO a takaice wadda ke da alaka da rundunar RSF, ta musanta zargin cewa dakarun RSF ne suka kaddamar da harin, tana mai cewa dakarun gwamnati na SAF ne suka kaddamar da harin ta sama kan jerin gwanon motocin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kaddamar da
এছাড়াও পড়ুন:
Libya Ta Tasa Keyar Baƙin Haure Yan Kasar Sudan 700 Zuwa Kasarsu
Gwamnatin Libya ta tasa keya daruruwan baƙin haure ‘yan ƙasar Sudan 700 zuwa ƙasarsu da yaƙi ya ɗaiɗaita, A cewar mahukuntan, waɗannan mutanen sun yi hijira zuwa Libya ne domin gujewa yaƙi da talauci, inda suke neman hanyar tsallakawa zuwa Turai.
A cewar huƙumar kula da baƙin haure, an kori mutane 700 daga Libya da aka kama a tsakiya da kudu maso gabashin ƙasar, inda aka tura su zuwa Sudan a ranar Juma’ar da ta gabata ta ƙasa.
Bayanin ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka korar na ɗauke da cututtuka masu yaɗuwa kamar su hepatitis da cuta mai karya garkuwar jiki, wasu kuma an tura su ne saboda laifuffuka ko kuma dalilan tsaro.
Korar ta zo ne a lokacin da mahuƙuntan ke ci gaba da yaƙi da safarar mutane a gabashin Libya, wanda ke ƙarƙashin ikon kwamandan sojoji Khalifa Hiftar.
A makon da ya gabata, masu tsaron gaɓar teku a gabashin Libya sun kame wani jirgin ruwa da ke ɗauke da baƙin haure 80 da ke neman zuwa ƙasashen ƙetare, a gabashin birnin Tobruk.
Yaƙin da hukumomin ke yi sun haɗa da kai hare-hare kan wuraren da ake safarar mutane a gabashi da kudancin Libya. A farkon wannan watan, an ƙwato baƙin haure ‘yan Sudan 104, ciki har da mata da yara, da aka tsare a gidan da ake tara mutane da ake fataucin su a birnin Ajdabiya, mai nisan kilomita 800 daga babban birnin Tripoli, a cewar ƴan sa kai na yankin.
Libya ta zama hanyar wucewa ga mutanen da ke guje wa yaƙi da talauci a yankunan gabas ta tsakiya da Afirka, inda suke neman rayuwa mai kyau a Turai.
Masu safarar mutane sun ci gajiyar rashin kwanciyar hankali a Libya tsawon shekaru goma, inda suke shigar da baƙin haure ta iyakokin ƙasar da suka haɗa da ƙasashen Chadi da Nijar da Sudan da Masar da Aljeriya da kuma Tunisiya.