Jami’an Tsaron A Nan Iran Sun Kama Yan Kungiyar ISIS Kafin Su Aiwatar Da Hare-Hare
Published: 4th, June 2025 GMT
Jami’an Yansanda masu kula da ayyukan ta’addanci da kuma hana aukuwarsu a nan Iran sun sami nasarar kama wasu yan kungiyar ISIS 13 a duk fadin kasar daga ciki har da shugabansu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Saeed Montazer al-Mahdi kakakin rundunar FARAJA mai kula da fada da yan ta’adda yana fadar haka.
Labarin ya kara da cewa an kama yan ta’addan na ISIS a biranen Tehran, Qum, Esfahan da kuma Albus. Kuma an kama tare da su kayakin aiki wadanda suka hada da damarar boma bomai na kunan bakin waje da kuma jakunan da ake ratayawa a baya cike da abubuwan Facewa. Kakakin rundunar FARAJA y ace suna dauke da karin bayani nan gaba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Uranium A Cikin Kasarta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa; Ba zai yiwu Iran ta iya yin watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Har yanzu ba a daina sarrafa sinadarin Uranium ba a Iran, duk da irin barnar da hare-haren Amurka ya yi wa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran.
A wata hirarsa da Fox News, Araqchi ya amsa tambayoyi kan cewa: “Shin shirin inganta sinadarin Uranium a Iran ya dawo? Shin har yanzu yana ci gaba, ko kuma barnar da aka yi wa Iran ya yi tsanani har ta kai ga dakatar da shi gaba daya?” Araqchi ya amsa da cewa; “Ba a daina bainganta sinadarin ba, duk da cewa barnar ta yi tsanani, amma duniya ta sani Iran ba za ta iya yin watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba saboda muhimmancinsa, domin wannan nasara ce ta masana kimiyyar kasar, kuma a halin yanzu abin alfahari ne ga kasa, kuma inganta sinadarin Uranium yana da matukar muhimmanci ga Iran.”
Da yake amsa tambayar cewa: “Mene ne dalilin da ya sa Iran ba za ta shigo da sinadarin uranium da ake inganta shi daga waje ba kamar yadda wasu kasashe ke yi? Araqchi ya ce: “Saboda wannan nasara ce ta ilimi, nasara ce da kasar Iran ta samu, to me ya sa za mu shigo da shi daga waje, duk da za ta iya samar da kanta?”.