An Kama Magidanci A Bauchi Bisa Zargin Lalata Da Agolarsa
Published: 8th, June 2025 GMT
PPRO ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana auren mahaifiyar wanda aka cutar (da sakaya sunanta).
“An bayyana cewa ya yi lalata da yarinyar a lokacin da mahaifiyarta ke barci, yana shiga dakinta kuma yana aikata abubuwan da ba su dace ba a lokuta da dama.
“Wakil ya ce, “Yarinyar na shan wahala amma duk da haka ta kame bakinta sai da lamarin ya ta’azzara sannan ta fada wa makwabta, wanda hakan ya kai ga daukar matakin kama wanda ake zargi da aikata laifin,”
Ya ce a lokacin da ake yi masa tambayoyi an ruwaito wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
“An kwashe wanda abin ya rutsa da shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa da kulawa.
“Kwamishanan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu ya bayar da umarnin mika karar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi, daga nan kuma za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria