Kididiga Ta Nuna Yadda Kasar Sin Ke Samun Bunkasar Tattalin Arzikin Teku
Published: 10th, June 2025 GMT
Kididdigar ci gaban tattalin arzikin bangaren tekun kasar Sin, wadda take muhimmin ma’aunin duba ci gaban tattalin arzikin tekun kasar, ta karu da kashi 2.3 bisa dari a bisa mizanin shekara-shekara, inda ta koma zuwa kaso 125.2 a shekarar 2024, lamarin da ya nuna cewa an samu ci gaba mai karfi a fannin teku.
Ma’aikatar albarkatun kasa ce ta fitar da wannan kididdigar a jiya Lahadi albarkacin bikin ranar teku ta duniya.
Bayanai sun nuna cewa, an inganta tsarin sabbin masana’antun bangaren teku na kasar Sin a shekarar 2024, tare da samun ci gaba a fannin fasahar kere-kere. Haka nan, an samu habakar amfani da tattalin arzikin teku da inganta karamin sashen kididdigar da ake yi da kaso 131 cikin dari a shekarar 2024, wadda ke nuna sashen ya karu da kaso 1.8 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
Kididdigar ma’aikatar ta kuma nuna cewa, hada-hadar masana’antun bangaren teku masu tasowa da aka samu a bara ta karu da kaso 7.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara. Bugu da kari, kamfanonin da ke da alaka da teku sun samu makudan kudi har yuan biliyan 11.4 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.58 ta hanyar kudin da ake warewa a tsarin mallakar da kamfanoni masu zaman kansu ga gwamnati, watau IPO, wanda hakan ya kai kashi 17 cikin dari na jimillar kudin tsarin IPO na kasar Sin, inda ya kara nuna karfin harkokin kasuwannin hannun jari na bangaren tekun kasar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: bangaren teku
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: Taro Tsakanin Iran Da Tawagar Kasashen Turai Dama Ce Ta Gyarar Tunanin Tarai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron Istanbul wata dama ce ta gyara matsayar Turai kan shirin makamashin nukiliyar Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, ya yi la’akari da taron na yau tsakanin Iran da kasashe uku mambobin kungiyar hadin gwiwa ta JCPOA a matsayin wata muhimmiyar dama ta gyara ra’ayoyinsu da gwada hakikaninsu kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran.
A cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labaran IRNA, Isma’il Baqa’i ya bayyana fatansa na cewa wadannan kasashe uku za su yi amfani da wannan damar wajen gyara tsarin da suka bi a baya wanda bai dace ba, wanda ya lalata martabar Turai da matsayin tattaunawa, tare da mayar da ita a matsayin yar wasa maras tushe.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana takaicinsa game da matsayin kasashen Turai uku na nuna son zuciya dangane da wuce gona da iri da gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka dauka kan kasar Iran – wadanda suka gabatar da wadannan kasashe uku ga duniya a matsayin tushe haifar da hargitsi da mara wa ta’addanci gindi. Ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a baya ta yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da irin wadannan matsayar da ba ta dace ba, kuma tabbas a taron na yau Juma’a za a isar da zanga-zangar Iran dangane da hakan ga bangarorin Turai, kuma za a bukaci su yi karin haske.