Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 5th, June 2025 GMT
Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan filin jirgin saman Lod da ke Jaffa da aka mamaya da jiragen sama biyu marasa matuka ciki
Sojojin Yemen sun sanar da kai wani farmakin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma nuna tsananin Rashin amincewa da kisan kiyashin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwansu a zirin Gaza.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, inda ta ce farmakin da rundunar sojin saman Yemen ta kai da jiragen saman yaki marasa matuka ciki kirar Yaffa guda biyu, ya samu nasarar cimma burin da ake bukata.
Rundunar sojin ta yi nuni da cewa: A daidai lokacin da mahajjatan dakin Allah suke shirin tsayuwa a Arafat, suna tasbihi da gode wa Allah, ana ci gaba da zubar da jinin ‘yan uwansu a Gaza, ba tare da wani mataimaki ko mai ceto daga al’ummar musulmi ba, duk kuwa da irin karfin da za a iya kawo karshen wannan kisan kiyashi, wanda duniya ba ta taba ganin irinsa ba.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka.
“Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem.
Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen duniya da gaza aiwatar da dokokin kasa da kasa, yana mai cewa, “Shiru da kasashen duniya suka yi, abin Allah wadai ne ga gwamnatocin kasashen duniya, musamman na kasashen musulmi da larabawa.
Da yake ishara da kiraye-kirayen baya-bayan nan da kasashe sama da ashirin suka yi na a dakatar da yakin, Sheikh Qassem ya yi ishara da cewa irin wadannan kalamai da cewa ba su isa ba ko kadan, Ya ce, “bai isa ba a ce kasashe 25 sun yi kira da a dakatar da yakin Gaza, wannan furucin kadai bai wadatar ba.
Sheikh Qassem ya yi kira da a kakaba takunkumi kan “Isra’ila”, da gurfanar da su a gaban shari’a, da kuma dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.