Shugaban Xi Da Takwaransa Na Myanmar Sun Mikawa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 75 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya
Published: 9th, June 2025 GMT
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Myanmar Min Aung Hlaing, sun mikawa juna sakon murnar cika shekaru 75, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, cikin shekaru 75 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Myanmar, bangarorin biyu sun bi ka’idoji 5 na zama tare cikin lumana, da kuma tunanin Bandung, da sada zumunta, da zurfafa hadin gwiwar samun moriyar juna, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, sun kuma kasance abun koyi a fannin sada zumunta tsakanin kasa da kasa.
Ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da kokari tare da Myanmar, don gaggauta raya hadin gwiwa mai inganci bisa shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”, da aiwatar da kiran raya kasashen duniya, da kiran kiyaye tsaron duniya, da kiran raya al’adun duniya, da kuma sa kaimi ga raya makomar bai daya ta Sin da Myanmar, don kara cin gajiyar al’ummun kasashen biyu baki daya.
A nasa bangare, shugaba Min Aung Hlaing ya ce, Myanmar ta gamu da girgizar kasa mai tsanani, kuma gwamnatin kasar Sin da jama’arta sun samar da gudummawar jin kai cikin hanzari, wanda hakan ya shaida cewa, al’ummun kasashen biyu suna sada zumunta mai zurfi, da nuna goyon baya ga juna. Kazalika, Myanmar tana jinjinawa kasar Sin bisa goyon bayan da take nuna mata, a turbarta ta kokarin neman samun zaman lafiya, da sulhunta kabilunta, da bunkasa tattalin arziki a kasar, kana tana son sa kaimi ga yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, don raya dangantakar abokantaka mai karfi da moriyar juna a tsakaninsu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Taron Kolin Sin Da EU Zai Bayar Da Damar Zurfafa Hadin Gwiwar Sassan Biyu
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya baki daya.
Guo Jiakun, ya jaddada muhimmancin taron, kasancewar ya zo a gabar da harkokin cudanyar kasa da kasa ke fuskantar yanayi na tangal-tangal, da ma karuwar daukar matakan kashin kai daga bangare guda, da kariyar cinikayya.
Ya ce, hadin gwiwar sassan biyu, ya haifar da manyan nasarori a baya, wanda hakan ya bunkasa ci gaba da daukakarsu, tare da samar da tarin alfanu ga jama’arsu da yawanta ya kai biliyan biyu, kana ya samar da babbar gudummawa ga raya zaman lafiya, da ci gaban duniya baki daya. Kazalika, hadin gwiwar sassan biyu ya zamo misali na hadin gwiwar cimma moriyar juna, a sabon zamani na dunkulewar tattalin arzikin duniya.
Daga nan sai ya bayyana aniyar kasar Sin ta yin aiki tare da EU, wajen cimma nasarar taron, matakin da zai aike da kyakkyawan sako ga duniya, game da aniyarsu ta hada karfi da karfe, wajen kafa hadin gwiwa mai karfin gaske, da daga martabar cudanyar mabambantan sassa, da bude kofa da aiwatar da hadin gwiwa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp