Bukukuwan sallah tare da Malta Guinness a Birnin Kano
Published: 6th, June 2025 GMT
A yayin da al’ummomi a fadin Najeriya ke shirin Sallar Idi, daya daga cikin manya-manyan bukukuwan Musulunci,
Kano, cibiyar al’adun arewacin Najeriya, na shirin gudanar da wani biki Mai kayatarwa wanda Malta Guinness, ɗaya daga cikin samfuran kayan sha Mai dandanon Dadi da yayi fice a ƙasar nan, zai ƙaddamar da wannan biki na kwanaki uku da nufin zurfafa ruhin al’umma ta hanyar raba alheri da kyaututtuka ga masu rabo.
An tsara shirin ba a matsayin nunin tallace-tallace ba amma a matsayin taron nunin al’adu da ke tattaro irin kade-kade, da wasan kwaikwayo na gargajiya don nishadantarwa.
Za’ayi wannan ruguntsumi ne, a Dakin taro na Ado Bayero Hall, dake Kano, daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Yuni, 2025.
A lokacin wannan shagali akwai gasar Mai rabo ka samu wato na raffle inda wasu iyalai zasu samu damar samun kyautar Ragon Layya a lokacin wannan ruguntsumi na Bikin baje kolin al’adun gargajiya don nishadantarwa da raya aladu alokacin Bikin Sallar babba.
Wannan gangami dai zai kunshi fitattun jaruman fina-finai irinsu Ali Nuhu, wanda ake yi wa kallon wata gada ta yaukaka al’ada atsakanin mutanen arewa, akwai kuma fitattun jaruman da suka hada da Chef Maah da Ali Nurudeen da zasu kasance awajen wannan shagali.
Shigarsu wannan ruguntsumi yana nuna mahimmancin shirin da dacewa da al’adu da kuma faɗakarwa yayin da suke ƙarfafa saƙon haɗin kai ga jama’a.
Malta Guinness’ yana ba da wani hoto ba kawai a matsayin masu tallafawa ba amma a matsayin mahalarta taron bunkasa al’adu yayin da Kano ke cikin bukukuwan murnar Idi,
Kar ku manta kyawawan abubuwan da aka raba – zasu zama abin farin ciki da kuma tunawa da alherin da Malta Guinness a tsawon lokaci.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Dan shekara 10 ya harbe mahaifinsa ɗan sanda a Anambra
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya.
Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47.
Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCCWannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa.
Sanarwar ta ce “a ranar Lahadi 15 ga watan Yuni, dan gidan wani jami’in dan sanda mai kimanin shekara goma da haihuwa ya harbe mahaifinsa har lahira ya kuma jiwa yayan sa mummunan rauni.
“Abin bakin ciki muna sanar da ku mutuwar jami’inmu mai mukamin sufeto, Okolie Amechi, bisa harbe shi da dansa ya yi a gidansa.
“Wannan ba karamin abin takaici ba ne da kaddara,” in ji sanarwar.