Wagner ta kawo karshe kasantuwarta a Mali bayan fiye da shekaru uku
Published: 8th, June 2025 GMT
Kamfanin sojojin haya na Rasha, Wagner, ya sanar da janyewarsa daga kasar Mali, abin da ya kawo kƙarshen fiye da shekaru uku na ayyukansa a wannan kasa ta Yammacin Afirka.
“Mun taimaka wa ‘yan kishin kasa wajen gina wata rundunar sojoji mai karfi da tsari, wacce za ta iya kare kasarsu.
Dukkan manyan biranen yankin sun koma karkashin ikon mahukuntan da ke da ikon tafiyar da harkoki a kasar,” in ji Wagner.
Kasar Mali, da ke yankin Sahel, ta sha fama da hare-haren ‘yan tawaye tun daga shekarar 2012, kuma sojojin dake mulki a kasar sun nemi taimakon Rasha bayan sun katse dangantaka da Faransa da sauran abokan hulda.
A farkon wannan shekarar, kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, da sojoji sukayi juyin mulki, sun fice daga kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka, inda suka kafa wata sabuwar kungiya mai suna AES.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.
Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.
Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp