Kasashen Da Sin Ta Bai Wa Jama’arsu Izinin Shiga Kasar Ba Tare Da Biza Ba Ya Karu Zuwa 47
Published: 10th, June 2025 GMT
Tun daga yau Litinin 9 ga watan Yuni, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bai wa ’yan wasu kasashe iznin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ciki har da Saudiyya, da Oman, da Kuwait, da Bahrain. Kawo yanzu, adadin kasashen da kasar Sin ta bai wa jama’arsu izinin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ya habaka zuwa 47.
Tun daga ranar 9 ga watan Yunin shekara ta 2025, zuwa ranar 8 ga watan Yunin shekara ta 2026, mutanen dake da takardar fasfo daga kasashen Saudiyya, da Oman, da Kuwait, da kuma Bahrain, idan suna so su shigo kasar Sin don yin kasuwanci, ko yawon bude ido, ko ziyartar iyalai da abokansu, ko kuma rangadin aiki na kasa da kwanaki 30, babu bukatar su nemi takardar biza na shiga cikin kasar wato “visa”.
Tuni a shekara ta 2018, kasar Sin ta aiwatar da irin wannan manufa ga Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Qatar, al’amarin da ya sa kawo yanzu kasar Sin ta aiwatar da wannan manufa ga dukkan kasashe membobin kungiyar GCC.
Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, karuwar yawan kasashen da kasar Sin ta bai wa jama’arsu izinin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ya shaida babbar niyyarta ta fadada bude kofa ga kasashen waje, kana, Sin za ta ci gaba da kyautata manufofin shiga cikin kasar, da kara habaka yawan kasashen da manufar ta shafa, ta yadda baki ’yan kasashen waje za su kara jin dadin kayayyaki, da kasuwanni, gami da hidimomin da aka samar musu a kasar ta Sin, kuma kasashe daban-daban za su more ci gaba tare da kasar Sin bisa hadin-gwiwar da suke yi. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: shiga cikin kasar kasar ba tare da takardar biza kasar Sin ta da takardar
এছাড়াও পড়ুন:
An Watse A Taron EU Da China Saboda Ricikin Kasuwanci Da Siyasa Tsakaninsu
An takaita taro tsakanin kasashen turai da China a birnin Beijin zuwa ranar Alhamis kadai bayan da bangarorin biyu sun sami sabani a tsakaninsu kan al-amuran kasuwanci.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron har na tsawon kwanaki uku amma kwotsom sai kasar China ta bukaci a takaita taron zuwa jiya Alhamis kadai.
A nata bangaren shugaban tarayyar ta turai Ursula von der Leyen ta bayyana cewa, kasat China ce kadai take amfani da tsarinn kasuwancin da ke tsakanin bangarorin biyu, ta bada misali da cewa bambancin ribar da china take samu a cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai Euro biliyon 305.8 ko dalar Amurka biliyon 360 a shekarar da ta gabata kadai. Sannan harkokin kasuwanci a tsakanin Eu da China yana karuwa kamar yadda bambanci da rashin daidaito yake karuwa. Don haka tace dole ne a sauya tsarin. Amma gwamnatin kasar China ta ce rashin daidaito a harkokin kasuwanci tsakanin bangarorin biyu ba daga kasar China ya taso ba, saboda kasashen Eu suna harkokinnwasuwanci da kasashen duniya da dama. Shugaban kasar China Xi Jinoing ya bukaci kungiyar EU ta gyara harkokin kasuwancinta da kanta.