Sin Ta Yi Fatali Da Ikirarin Amurka Cewa Ta Karya Yarjejeniyar Tattaunawar Geneva
Published: 4th, June 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, a yau Talata ya yi watsi da ikirarin da Amurka ta yi na cewa kasar ta Sin na karya yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin kasashen biyu a tattaunawar tattalin arziki da kasuwanci da aka yi a Geneva, inda ya bukaci Amurka da ta daina yada labarun kanzon kurege.
A yayin taron manema labarai na yau da kullum, Lin ya bayyana cewa, kasar Sin ta dauki matakin da ya dace, tare da daukar yarjejeniyar da aka cimma a shawarwarin Geneva da muhimmanci, tare da aiwatarwa yadda ya kamata.
Yanzu-yanzu: JUSUN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Fara A Faɗin Ƙasa Baki Ɗaya Sallah: Gwamnatin Kebbi Ta Raba Naira Miliyan 337 Ga Mata 11,229Bugu da kari, Lin ya ce, Amurka ta yi matukar kawo cikas ga yarjejeniyar, ta hanyar daukar matakan nuna wariya da dama a kan kasar Sin, ciki har da fitar da tsare-tsaren hana fitar da kayayyakin fasahar sadarwar kirkirarriyar basira, watau AI Chip, da dakatar da sayar da zayyanar manhajar kayayyakin fasahar ta AI Chip ga kasar Sin, da kuma sanar da soke biza ga daliban kasar Sin.
Yayin da yake jaddada cewa matsin lamba da tilastawa ba su ne hanyoyin da suka dace na mu’amala da kasar Sin ba, jami’in ya bukaci Amurka ta mutunta hakikanin gaskiya, da dakatar da yada labarun kanzon kurege, kana ta gyara kura-kuranta, da kuma daukar kwararan matakai na kiyaye yarjejeniyar da aka cimma yayin tattaunawar Geneva. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran Tace Tawagar Kwararru Daga Hukumar IAEA Zata Ziyarci Kasar Nan Ba Da Dadewa Ba
Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da daewa ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka.
Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin kasar Iran kan yadda mu’amalar hukumar zata kasance da Iran. Gharibabadi ya bayyana cewa idan kasashen yamma sun yi kokarin amfani da shrin SnapBack na yarjeniyar JCPOA zasu gamu da maida martani mai tsanani, sannan ya kara da cewa mu’amala da hukumar IAEA da kasar Iran zata sauka saboda amfani da karfi kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran wanda Amurka da HKI suka yi a kallafeffen yaki na kwanaki 12 a cikin watan yunin da ya gabata.
Mataimakin ministan ya bayyana cewa, Iran zata ci gaba da kasancewa cikin yarjeniyar NPT mai hana yaduwar makaman nukliya a duniya. Amma dokar da Majalisar dokokin kasar Iran ta kafa ta jingine hulda da hukumar IAEA ya sa Iran za ta sanya hulda da hukumar takaitacce shi dimma tare da wasu sharudda guda biyu. Gharib abada ya fadawa yan jaridu a birnin NewYork a ranar Laraban da ta gabata kan cewa tawagar ba zata kai ziyara cibiyoyin makamashin nukliya na kasar ba. Sannan ya kammala da cewa hukumar makamashin nukliya na kasar Iran na lissafin irin asarorin da hare-hare Amurka suka yiwa cibiyoyin Nuklkiyar nkasar A Esfahan, Natansa da kuma Fordo.