Aminiya:
2025-10-16@01:29:04 GMT

Sallah: Gwamna Inuwa ya yi kiran sadaukarwa da haɗin kai

Published: 6th, June 2025 GMT

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aika da sakon taya murnar Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi, yana kira gare su da su rungumi darajoji na sadaukarwa, biyayya da hakuri irin wanda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna.

A wata sanarwa da Daraktan Yada labarai na gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Gwamnan ya yi kira da a yi addu’o’in zaman lafiya da haɗin kan Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.

Ya jaddada muhimmancin nuna soyayya, tausayi da zama mai ƙyau da maƙwabta a rayuwar yau da kullum.

“Yayin da muke murnar Babbar Sallah, mu yi tunani kan abin da take nufi biyayya, sadaukarwa da ƙwarin gwiwa,” in ji Gwamna Yahaya, yana mai ƙarfafawa al’umma da su ci gaba da tallafa wa shugabanci a matakai daban-daban.

Gwamnan ya yaba wa shugabannin gargajiya da na addini bisa goyon bayansu tare da tabbatar da kudirinsa na kammala ayyukan ci gaba da aiwatar da sabbin manufofi masu alfanu.

Haka kuma, ya taya Alhazai Musulmi murnar kammala aikin Hajji, yana yi musu addu’ar dawowa lafiya da samun albarkar wannan ibada.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Babbar Sallah Gwamna Inuwa Yahaya

এছাড়াও পড়ুন:

Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba waɗanda ke kashe mutane ba gaira ba dalili.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne a yau a wajen bikin yaye sabbin jami’an tsaron cikin gida (Community Watch Corps – CWC) guda 100, a karo na uku da aka gudanar a Katsina.

Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Radda, ya karyata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yada cewa gwamnatinsa tana tattaunawa da ’yan bindigar da ke ɓoye a dazuka.

A cewarsa: “Babu wata tattaunawa ko sasanci da gwamnati ke yi da ’yan ta’adda. Wadannan labarai ƙarya ne, kuma manufar gwamnati ita ce kawo ƙarshen ta’addanci, ba yin sulhu ba.”

Sai dai ya ce, gwamnati za ta iya rungumar zaman lafiya idan waɗannan mutane sun yi tuba na gaskiya, tare da miƙa wuya, suka daina zubar da jini.

Gwamna Radda, ya bayyana cewa horar da jami’an CWC wani ɓangare ne na sabuwar dabarar gwamnati ta inganta tsaro, musamman a yankunan karkara da suka fi fama da hare-haren ’yan ta’adda.

Tun bayan ƙaddamar da Katsina jami’an tsaron a shekarar 2023, an horar da dubban matasa sama da 2,400 daga sassa daban-daban na jihar.

Wadannan jami’ai na aiki tare da ’yan sanda, sojoji, da jami’an Sibil Difens, don taimakawa wajen samun bayanan sirri da hana hare-haren ’yan ta’adda.

Gwamnan, ya ce horar da waɗannan jami’ai zai taimaka wajen kawo ƙarshen satar mutane da hare-haren ’yan bindiga, tare da tabbatar da zauna lafiya a Jihar Katsina.

Ya kuma yi kira ga al’umma su bai wajami’an tsaro haɗin kai, su rika bayar da bayanai domin ganin an samu nasara a yaki da ta’addanci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Inuwa ya naɗa sabbin shugabanni a ma’aikatar lafiya ta Gombe
  • Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 
  • Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda
  • Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles
  • Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan
  • Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP
  • Jihar Kano Na Aikin Gyaran Cibiyoyin Lafiya Da Za Su Yi Gogayya Da Na Ƙasashen Duniya
  • Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin
  • Gwamnan Enugu Peter Mbah da kwamishinoninsa sun koma APC
  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP