Aminiya:
2025-07-23@23:47:59 GMT

Musulman Kudancin Kaduna sun yi taron addu’ar zaman lafiya

Published: 5th, June 2025 GMT

Al’ummar Musulmin yankin Kudancin Kaduna, sun shirya taron addu’a na musamman a sakatariyar karamar hukumar Sanga da ke Gwantu, Jihar Kaduna, kan neman zaman lafiya.

A yayin taron dai Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya jaddada kudirin rundunar sojin Najeriya na dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin kasar tare da yin kira ga ’yan kasa da su mara wa kokarin hadin kai da ci gaban kasa baya.

Janar Musa wanda Rear Admiral Ibrahim Aliyu Shettima ya wakilta, ya ce zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaba da bunkasar kasa. Ya bukaci ’yan Najeriya baki daya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba, da su bayar da gudummawarsu wajen gina kasa.

Barazanar Yajin Aiki: Abuja da wasu jihohi 3 za su faɗa cikin duhu A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates

Taron addu’ar dai an shirya shi ne da nufin karfafa zaman tare cikin fahimta da hadin kai tsakanin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba daga kowace kabila a yankin, ya hada limamai da malamai daga kananan hukumomin Sanga, Kaura, Jema’a, Kachia, Kagarko, Kauru, Jaba, Kajuru da Chikun.

A jawabin sa, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Jama’a kuma shugaban al’ummar Musulmin Kudancin Kaduna da suka gudanar da addu’ar, Sheikh Muhammad Kabir Qassim, ya nuna damuwarsa kan rikice-rikicen kabilanci da na addini da suka addabi yankin tsawon shekaru, lamarin da ya ce ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

“Allah ya albarkaci Kudancin Kaduna da kasar noma mai albarka, wacce za a iya noma amfanin gona ba kawai don amfanin gida ba, har ma don fitar da shi kasashen waje. Amma babu wani ci gaba da za a samu idan babu zaman lafiya da tsaro,” in ji shi.

Ya yi kira ga daukacin mazauna yankin da su hade kai wajen dawo da martabar yankin da ta lalace tare da jaddada cewa hadin kai ne makamin jawo masu zuba jari da samar da damarmaki ga matasa.

Malamin ya nuna godiyarsa ga kokarin Janar Christopher Musa na dawo da zaman lafiya, yana mai cewa kudirinsa na tattaunawa da sulhuntawa zai taimaka wajen bude sabuwar hanyar ci gaba a Kudancin Kaduna da Najeriya baki daya.

Sauran masu jawabi a wajen taron sun jaddada muhimmancin hadin kan addinai da hadin gwiwar al’umma wajen magance matsalolin tsaro, tare da daukar alkawarin ci gaba da yin addu’o’i don samun zaman lafiya da hadin kai a fadin kasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Zaman lafiya zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Hana Natasha Zaman Majalisa Barazana Ne Ga Dimokuraɗiyya — CLO

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Kano Za Ta Hada Gwiwa FMBN Don Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi
  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  • Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
  •  Iraki Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Akan Dakarun Sa Kai Na” Hashdus-sha’abi”
  • Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
  • Hana Natasha Zaman Majalisa Barazana Ne Ga Dimokuraɗiyya — CLO
  • Taron Kolin Sin Da EU Zai Bayar Da Damar Zurfafa Hadin Gwiwar Sassan Biyu
  • Asibitin ATBUTH za ta fara gwajin rigakafin zazzaɓin Lassa
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.