2025-09-17@23:24:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 31
«Huɗubar Ranar Arfa»:

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
Har ila yau, Lin ya ce matsayin kasar Sin dangane da rikicin kasar Ukraine bai sauya ba, cewa tattaunawa, da gudanar da shawarwari ne kadai hanyoyi mafiya dacewa na warware rikicin. Har kullum Sin na kan turbar adalci game da rikicin, tana kuma ci gaba da ingiza bukatar komawa teburin shawara tun barkewar rikicin....

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake. A cewar...
Har yanzu babu tabbaci ko zai iya buga wasan. Arsenal na fatan cewa Saka da Odegaard ba za su daɗe suna jinya ba. A kakar da ta wuce, Saka ya sha fama da rauni har ya yi watanni uku ba ya wasa. Sai dai a bana Arsenal ta ƙara wasu sababbin ‘yan wassan gaba kamar...
Ya kuma yi gargadin cewa, “Wannan ba lokaci ba ne da Arewa za ta naɗe hannunta tana kallo yayin da al’amura ke ci gaba da taɓarɓarewa, lamarin tsaro yana kara ta’azzara yayin da ake ci gaba da kwashe albarkatun yankin, ambaliyar ruwa na ci gaba da barazana, dole ne mu tashi tsaye mu hada...
Yakasai ya kawo misalin tattaunawa da aka yi da kamfanoni a kasar China lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, inda aka kawo tawaga Kano don duba yiyuwar saka hannun jari amma rashin wutar lantarki ya kawo cikas, ganin cewa dokar gwamnatin tarayya a wancan lokaci ta hana jihohi samar da wutar lantarki ta kansu. Ya bayyana roƙo...
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu zata fara tattaunawar kasa dangane da talauci da kuma rashin adalci a rabon arziki a kasar. Gwamnatin kasar ta ware kimani dalar Amurka miliyon 40$ don gudanar da tattaunawar. Inda ake saran dukkan mutanen Afrika ta kudu suna da damar bayyana ra’ayinsu dangane da wadannan matsaloli. Na talauci da rashin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya. Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan...
Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon...
Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea...
Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea...
A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka...
A ranar 27 ga Mayu, 2025, Indomie Arewa ta ƙara ɗanɗano da armashi a cikin tasowar yara. Babban kamfanin abincin tana alfaharin ƙaddamar da Indomie AI Career Generator, wata dandalin zamani irinsa na farkon da aka ƙirƙira don nuna irin baiwar da yara ke da ita ta hanyar ba su damar ganin makomarsu ta wata sabuwar...
Tawagar kasar Sin a taron birnin Geneva, ta shaidawa kungiyar cinikayya ta duniya WTO, cewa kasar ta fadada matakinta na rage harajin fito da take karba daga kasashe masu karancin karfin tattalin arziki, daga kaso 98 bisa dari zuwa kaso 100 bisa dari. A jiya Laraba ne tawagar ta Sin ta bayyana wannan albishir, inda...

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Cimma Daidaito Da Sin Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya
Zuzzurfar tattaunawa da ta wakana tsakanin tsagin Sin da na Amurka a birnin Landan, ta sa masu bayyana ra’ayoyin jin karfin gwiwa game da makomar shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Kuri’un jin ra’ayin jama’a na kafar CGTN ta kasar Sin, sun nuna yadda masu bayyana ra’ayoyi suka amince cewa, shawarwari sun...
Rashin wutar lantarki a Arewa maso Gabashin Najeriya ya tilasta wa jama’a da ’yan kasuwa zaman ɗari-ɗari da asarar dukiya, sakamakon aikin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ke yi na aikin sabbin turakun wutar lantarki. Rashin wutar, wanda ya fara daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, ya shafi layin wutar...
Sanatocin Arewa sun bayyana alhini da jimami kan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin ‘yan wasan Jihar Kano da ke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala a Jihar Ogun. A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Musa Yar’adua ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta miƙa...
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya. Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci. Harsunan huda uku na daga cikin karin harsunan duniya guda 34 da...
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu...
Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba. Da yake magana ta wayar...
Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da...
Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila...

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani...
Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su...
Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja. Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar...
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana...
Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna: Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan...
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa...
Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya...