Aminiya:
2025-06-14@00:57:54 GMT

Bom ya kashe masu yawon murnar sallah a Sakkwato

Published: 10th, June 2025 GMT

Kimanin mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya bayan tarwatsewar wani abun fashewa da ake zargi mayaƙan Lakurawa sun dasa a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato.

Aminiya ta ruwaito cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke kan babura na hanyarsu ta dawowa daga yawon bikin sallah a ƙauyen Gwabro.

Isra’ila ta ƙwace jirgin ruwa a hanyar kai agaji Gaza Sojoji sun kashe wani kwamandan ’yan ta’adda a Yobe

Bayanai sun ce an dasa abun fashewar ne a ƙarƙashin wata itaciya da ke zaman wurin hutawar dakarun sojoji a lokacin da suka fito sintiri a yankin.

Majiyiyo sun ce mutum shida sun mutu nan take yayin da ɗaya daga cikin wasu mata biyu yara da suka jikkata ta rasu washegari.

Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Tangaza, Alhaji Ghazzali Rakah ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa waɗanda abin ya shafa mazauna ƙauyen Zurmuku ne.

Wannan dai ba shi na farau ba, domin kuwa a watannin da suka gabata sojoji da dama sun rasu sakamakon tashin abin fashewa a karamar hukumar.

Har yanzu dai matsalar tsaro babbar damuwa ce a wasu sassan Jihar Sakkwato, inda mazauna ke ci gaba da kiran mahukunta da su ƙara jajircewa wajen daƙile ta’adar masu tayar da ƙayar baya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Babbar Sallah Jihar Sakkwato

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴansanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ceto Mutane 11 A Delta Da Katsina

Rundunar Ƴansandan Nijeriya, tare da haɗin gwuiwar sauran hukumomin tsaro, ta samu nasarar cafke mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ceto mutane 11 da aka sace a jihohin Delta da Katsina. Wannan na cikin ƙoƙarin ci gaba da yaƙi da miyagun laifuka a faɗin ƙasa.

A jihar Katsina, an daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane a ranar 8 ga Yuni, 2025, a hanyar Danmusa zuwa Mara Dangeza, inda jami’an haɗin gwuiwa suka yi artabu da ‘yan bindiga. Bayan musayar wuta mai tsanani, jami’an suka tilasta masu laifin guduwa da raunukan harbi tare da kuɓutar da mutum 11 da suka sace ba tare da raunuka ba.

Yanzu-yanzu: Gwamnan Delta Oborevwori Ya Fice Daga PDP Zuwa APC Kocin Kano Pillars Usman Abdullahi Ya Ajiye Aikinsa

A jihar Delta, jami’an CP-Special Assignment sun cafke wani Abubakar Hassan, wanda ake zargin jagoran gungun masu garkuwa da mutane ne da ke aiki a jihohi da dama. Bayan gudanar da bincike, ya jagoranci jami’ai zuwa maboyarsu a dajin Ozoro, inda aka ƙwato bindigogi AK-47 guda biyu da harsasai. Hakanan, wani direba, Obi Ezekiel, ya shiga hannu yayin da aka gano bindiga ƙirar gida da alburusai a motarsa.

Babban Sufeton Ƴansanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya yaba da ƙwarewa da kwazon jami’an tsaro a waɗannan ayyuka, tare da jan hankali cewa rundunar zata ci gaba da gudanar da irin wadannan farmaki don tabbatar da cewa babu mafaka ga masu aikata laifi a duk faɗin Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu
  • Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi
  • Ƴansanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ceto Mutane 11 A Delta Da Katsina
  • Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya
  • Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna
  • Sojoji sun kashe kasurguman ’yan bindiga 3 a Zamfara
  • Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara
  • An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato
  • An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato 
  • An kashe mutum 15 a sabbin hare-hare a Filato