Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan.

Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata.

A makon da ya gabata, rundunar ta kashe aƙalla ‘yan ta’adda 20 a wani samame da aka kai Garin Mani, da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Wannan farmaki ya biyo bayan luguden wuta da aka riƙa yi wa ‘yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka.

Shugaban sojin ya ce motsa jiki abu ne da ya zama dole ga dukkanin ma’aikata, kuma babu wanda zai samu ƙarin girma ba tare da cikakken lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa ba.

Don haka, ya amince a gina sababbin wuraren motsa jiki a sansanonin rundunar Sojin Sama da kuma siyan sabbin kayan motsa jiki don raba wa sassan rundunar sama da 22.

Ya bayyana cewa aikin motsa jikin ba wai motsa jiki kawai ba ne, amma yana nuna karfi da daidaito da kuma ƙudirin rundunar wajen kare Nijeriya.

Ya buƙaci dakarun su kasance masu jajircewa da haƙuri domin cimma zaman lafiya.

Wannan aikin motsa jiki ana yin sa ne sau uku a shekara a dukkanin sassan rundunar Sojin Sama domin ƙarfafa jiki, haɗin kai da kuma nuna wa jama’a da maƙiya cewa rundunar Sojin Sama ta kasance cikin shiri, kuma za ta ci gaba da kare Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yan bindiga Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
  • Bida Poly ta kawo sojoji su kula da jarrabawar ɗalibai
  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara