Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kashe Falasdinawa Wadanda Suke Jin Yunwa A Gaza
Published: 4th, June 2025 GMT
Gwamnatin kasar Amurka wacce ta bude cibiyoyin rarraba kayakin Agaji a Gaza, ta ce zata rufe cibiyoyin zuwa ranar Alhamis mai zuwa don sake tsara ayyukan Rabomn. Majiyar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda sojojin yahudawan suna kashe falasdinawa wadanda suke fama da yunwa a lokacinda suka iso cibiyoyin raba abincin ko kuma suka hau kan hanyar zuwa karban abincin.
Labarin ya kara da cewa a jiya Talata kadai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa mayunwata 27 a kokarinsu na karban abinci.
Sannan a yau Laraba ya zuwa lokacin bada wannan labarin sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 32 a hare-haren da suka kai kan yankuna daban-daban a Gaza.
Majiyar ta kara da cewa Palasdinawa 95 ne sojojin yahudawan suka kai ga shahada a cikin sa’o’I 24 da suka gabata a gaza, sannan wasu 440 kuma suka ji rauni.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya zuwa yanzu Falasdina 54,607 ne suka yi shahada a Gaza, kuma tana ci gaba da kara kashewa ba wanda ya isa ya yi magana a duniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sojojin yahudawan
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Na Isra’ila Da Makami Mai Linzami Nau’in Flasdinu
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin tashi da saukar jiragen sama na Lod da makami mai linzami nau’in ‘Palestine 2’
Dakarun sojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani harin soji na musamman da aka kai kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami kirar “Palestine 2”.
A cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin jiya, Rundunar Sojin Yemen ta bayyana cewa: Farmakin ya sanya miliyoyin garken yahudawan sahayoniyya tsere zuwa matsuguni karkashin kasa tare da dakatar da ayyukan tashar jirgin sama.
Sanarwar ta ce harin da aka kaiwa filin jirgin sama na Lod nasara ce ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma mujahidansu, da kuma mayar da martani ga kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya suka yi a zirin Gaza.
Sanarwar ta yi kira ga daukacin al’ummar Larabawa da na Musulunci da su fito kan tituna “don nuna goyon bayansu ga ‘yan uwansu a Gaza, saboda yadda suke fuskantar zalunci da wuce gona da iri na killacewa.