Leadership News Hausa:
2025-06-06@14:53:05 GMT

Hajjin Bana: Falalar Tsayuwar Arfa

Published: 5th, June 2025 GMT

Hajjin Bana: Falalar Tsayuwar Arfa

Sannan Annabi (SAW) ya ce “Babu wata rana mafificiya a wajen Allah kamar Ranar Arfa”, haka nan kuma ragowar kwanakin da ke cikin 10 na farkon watan nan, Ranar Arfa ta ninninka su falala. Don a wannan ranar ce Annabi (SAW) ya ce Ubangiji yana sauka zuwa saman duniya (Kamar yadda ya dace da Shi (SWT). Ire-iren waɗannan Hadisan ne ake ce musu “Mutashabihai”.

Ana kawo bayanansu ne ta yadda za a yi mana kwatance amma ba kamar yadda ma’anar lamarin yake a hulɗar da ke tsakaninmu ba.
Wajibi ne yin imani da Hadisan don rashin yin imani da su ridda ne, amma ba kuma a riƙa fassarawa da yadda ƙananan ƙwaƙwalenmu ke ɗaukawa ba. Duk wanda ya ce zai fassara da ƙaramin hankalinsa, to wannan ya sa wasa a cikin sha’anin Allah (SWT).
Hadisin ya ci gaba da cewa “Ubangiji yana sauka a saman duniya sai ya yi alfahari da mutanen doron ƙasa. Yana kallon mutanen yana wa Mala’iku alfahari da su cewa ku kalli bayina, sun zo mun da birkitaccen gashi masu ƙura-ƙura, ga su sun yini, sun zo mun daga nesan duniya suna neman rahamata, ba su ga azabata ba.” Munzir ya ce Abu Ya’ala, Bazzaru, Ibn Khuzaima da Ibn Hibban suka ruwaito Hadisin. Amma lafazin da aka ruwaito da shi kuwa, na Ibn Mubarak ne daga Safyanus Sauri, shi kuma daga Zubairu bin Aliyin daga Anas bin Malik (RA).

Ma’anar kai ya yi ƙura-ƙura, ko da gashin mutum bai yi ƙura ba, Allah zai ba shi ladan, shi dai ya kasance ya kiyaye abubuwan da Shari’a ta ce ma sa kar ya yi. A kan haka ne ya sa ba a so a riƙa yin kwalliya bayan wanda aka yi a yayin ɗaukan harami.

Annabi (SAW) ya ce ba a taɓa ganin wata ranar da ake ‘yantar da bayi daga barin shiga wuta kamar Ranar Arfa ba. Duk zunubin da aka yi a shekara, rannan Allah yana zubar da shi.

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji

An karɓo kuma daga Ibn Mubarak, daga Safyanus Sauri, daga Zubairu bin Aliyin, shi kuma daga Anas bin Malik (RA) ya ce, “Annabi (SAW) ya tsaya a Arfa, da rana ta kusa faɗuwa, sai Annabi ya kira Bilalu ya ce ya sa mutane su yi shiru zai yi magana, sai Bilalu ya tashi ya ce wa jama’a; ku yi shiru ga Annabi (SAW). Sai Annabi (SAW) ya tashi yana kan raƙumi ya ce, “Ya ku taron mutane, yanzu Jibrilu ya zo mun ya gaishe ni, ya ce Ubangijina ya gafarta wa duk waɗanda suka zo Arfa ɗin nan, da waɗanda duk suka zo Mina (Mash’aril Harami) kuma Allah ya lamunce musu duk laifin da ke kansu”. Sai Sayyidina Umar bin Khaɗɗab (RA) ya miƙe ya ce “Ya Ma’aikin Allah, wannan namu ne da muka zo wannan Hajjin kawai? Sai Annabi (SAW) ya amsa ma sa da cewa “Naku ne kuma da duk waɗanda za su zo Arfa a bayanku har tashin ƙiyama”. Sai Sayyidina Umar (RA) ya ce “Alherin Allah yana da yawa kuma ya yi daɗi”. Imam Muslim da waninsa suka ruwaito.

Har ila yau, an karɓo wani Hadisin daga Ummul Mu’umina Aisha (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wata rana da Allah yake yawaita ‘yanta bayinsa daga wuta kamar Ranar Arfa. Ubangiji yana kusantowa (SWT) ga mutane har ya yi wa Mala’iku alfahari da su ya ce, “Me waɗannan mutane suke so ne?”.

Wannan yana nuna tambayar ta jindaɗi ce (yadda ya dace da Allah), saboda ai ya san abin da kowa yake so amma kuma sai ga shi (SWT) yana tambayar Mala’iku. Haƙiƙa ba ƙaramar falala ba ce a ce Allah ya yi alfahari da mutum, Alhamdu Lillah.

An karɓo Hadisi daga Abu Darda’i (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce, “Babu wata rana da ake ganin Shaiɗan a matsayin mafi ƙasƙanci da wulaƙanta da tunkuɗewa da fushi kamar Ranar Arfa”. Ba komai ya jawo ma sa wannan ba sai abin da yake gani na Rahamar Allah da take sauka.

Hatta shi kansa Shaiɗan yana zuwa Arfa, a maimakon shi ma ya samu yafiya a wurin Allah, sai kuma ya sake jibgan wani laifin saboda hassada a kan Rahamar da Allah yake wa bayinsa. Yana-ji-yana-gani, Allah zai yafe wa al’umma duk saɓon da ya ingiza su suka aikata.

Wannan baƙin cikin ma bai isa ba, tun da har ya yi hassada, ya ji baƙin cikin gafarar da Allah ya yi wa bayinsa, za a kuma tafi Mina bayan an sauko daga Arfa a jefe shi a can.
Ko kuma dama shi duk mai hassada idan ya ga wanda Allah ya baiwa ni’imar da yake baƙin ciki a kai; sai ya ji rashin lafiya ta taso ma sa. Abin da yake samun Iblis kenan. Al’umma za su taso daga Arfa cikin gafara kuma su je su jefe shi.

Haka nan, ya yi irin wannan baƙin cikin Ranar Badar. Da aka tambayi Annabi (SAW) irin baƙin cikin da ya yi a ranar, Annabi (SAW) ya ce “Iblis da ya ga Jibrilu yana jagorantar Rundunar Mala’iku, ba a taɓa ganin tsoro ya kama shi irin na rannan ba, har ma ya mance ya ce yana tsoron Allah”.

Allah ya amfanar da mu baki ɗaya, Albarkar Annabi (SAW).

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Arfa Kasa Mai Tsarki kamar Ranar Arfa alfahari da da Allah ya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Ya bayyana hakan ne a hukumance a ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar da ke Uyo, babban birnin jihar.

Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda

Wannan mataki ya biyo bayan wasu kwanaki da ya shafe yana nuna sha’awarsa na sauya sheƙa.

A wani taron jama’a da aka gudanar a Ikot Abasi, ya ce: “Lokaci ya yi da za mu motsa” domin a haɗa kai da Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta.

Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan shafe watanni uku yana tattaunawa da manyan mutane da masu ruwa da tsaki a jihar.

Ya nuna godiyarsa ga PDP saboda goyon bayan da suka ba shi, amma yanzu lokaci ya yi da zai ci gaba da tafiya gaba.

Ya bayyana cewa yana matuƙar ƙaunar Shugaba Bola Tinubu, kuma yana ganin Jihar Akwa Ibom za ta fi amfana idan tana aiki kafaɗa da kafaɗa da Gwamnatin Tarayya.

Gwamna Eno, ya sha alwashin cewa zai ci gaba da yi wa mutanen jihar aiki tuƙuru, ko daga wacce jam’iyya yake.

“Na kammala ganawa da jama’a a matsayin wanda kuka zaɓa, kuma na yanke shawarar komawa jam’iyyar APC,” in ji shi.

Gwamnonin jam’iyyar APC ne suka tarbe shi, ciki har da Gwamnan Jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma; Bassey Otu na Jihar Kuros Riba; Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas; da Dapo Abiodun na Jihar Ogun.

Sauran da suka halarta sun haɗa da Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta, Monday Okpebholo na Edo, da Francis Nwifuru na Jihar Ebonyi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
  • Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)
  • Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ga Mahajjatan Aikin Hajjin Bana A Kasa Mai Tsarki
  • Mahajjata Aikin Hajjin Bana Sun Tafi Tsayiwar Arafat A Yau Alhamis Don Fara Ginshikin Aikin Hajj
  • Mahajjata kusan miliyan biyu na hawan Arfa a Saudiyya
  • Hajjin 2025: Alhajin Kano Ya Rasu A Makka Kwana Ɗaya Kafin Arfa
  • Maniyyata na hawan Arfa a kasar Saudiyya
  • Darajar Hajojin Da Aka Fitar Waje Daga Birnin Shanghai Ta Kai Yuan Biliyan 629 Cikin Watanni Hudu Na Farkon Shekarar Bana
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Yi Tanadi Na Musamman Ga Alhazanta A Mina