Dalilin Rashin Fara Aikin Kamfanin Takin Zamani Na Gwamnatin Jihar Neja
Published: 7th, June 2025 GMT
“Gwamnatin ta yi hakan ne, sakamakon tabbatar da ganin an fara aiki a kamfanin daga nan zuwa karshen watan Mayun shekarar 2025.
“Gwamnatin Jihar da shude ce ta bai wa kamfanin kwangilar da kuma wani kamfani da ke Kasar Indiya aikin, inda gwamnatin ta zuba dala biliyan 12 a kamfanin,” in ji Hamza.
Sai dai, ya bayyana cewa; saboda kasancewar wasu dalilai, ba a samu cimma wata gagarumar nasarar a zo a gani ba a kan aikin.
Ya sanar da cewa, a watan da ya gabata ne, gwamnatin jihar ta sake yin nazari kan yarjeniyar ta baya da aka kulla, wadda kuma za a dawo, domin a ci gaba da yin aikin.
Babban Sakaren ya kara da cewa, manyan batutuwan da suka zama hummulhaba’isin dakatar da aikin su ne, kaluabalen rashin tsaro, amma yanzu, an sake yin nazari a kan sake dawo da ci gaba da aikin.
“An samar da daukacin Injinonin kamfanin, domin gudanar da aikin, amma kalubalen rashin tsaro ya jawo koma baya,” a cewar Babban Sakataren.
Ya yi nuni da cewa, idan aka fara gudanar da aikin, zai kara sanya wa manoman jihar samun wadataccen takin zamani, a kuma kan farashi mai rashusa.
Ita ma da take yi wa ‘yan jaridar karin bayani tun da farko, kwamishinan samar da bayanai da tsare-tsare, Binta Mamman ta bayyana cewa; an kara samar da tsaro a yankin, wanda hakan zai bai wa manoman jihar, damar komawa gonakinsu, domin fara aikin noma na bana.
“A shekarun baya, manoman jihar da dama, ba sa iya zuwa gonakinsu, domin yin noma, amma yanzu ba su da wata matsala ko fargaba wajen zuwa gonakin nasu, domin yin noma,” a cewar Binta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu.
A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000.
Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp