Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano
Published: 4th, June 2025 GMT
Wata kotu da ke unguwar Noman’s Land a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare fitaccen ɗan TikTok, Abubakar Kilina, a gidan gyaran hali har zuwa ranar 17 ga Yuni, 2025.
Wannan hukunci ya biyo bayan tuhumar da Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta shigar da ke zargin sa da aikata halaye da suka saɓa wa tarbiyya da al’adu Hausawa.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na yunƙurin hukumar na daƙile yaɗuwar rashin ɗa’a a kafafen sada zumunta, musamman TikTok.
“Mun ƙudiri aniyar daƙile duk wani abin da zai ci karo da tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci a Kano.
“Wannan matakin kotu yana nuna cewa ba za mu lamunci irin wannan hali daga matasa ba,” in ji Abba.
Mai shari’a Hajiya Halima Wali, wacce ta jagoranci zaman kotun, ta bayar da umarnin tsare Abubakar Kilina har zuwa ranar da za a ci gaba da sauraron ƙarar, bayan ya amsa dukkanin tuhume-tuhumen da aka karanta masa.
“Laifin da ake tuhumarsa da shi ya saɓa da doka, kuma ya amsa laifinsa kai tsaye. Dole ne mu ɗauki matakin da ya dace don hakan ya zama izina ga wasu,” cewar wata majiya daga kotun.
A cewar hukumar, ana zargin Kilina da yin shigar mata da kuma yin kalamai na nuna rashin tarbiyya a shafinsa na TikTok, wanda hakan ke kawo rashin ɗa’a da kuma tasiri mara kyau ga matasa.
“Mun daɗe muna faɗakarwa da gargaɗi. Amma yanzu lokaci ya yi da za mu ɗauki matakin doka domin dakatar da wannan mummunan lamari,” in ji Abdullahi Sani Sulaiman, jami’in yaɗa labarai na hukumar.
Hukumar tace fina-finai ta Kano ta ce wannan ba shi ne karon farko ba da ta ke kai matasa gaban kotu a kan irin waɗannan halaye.
A baya an samu wasu da aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya ko zaɓin biyan tarar Naira 100,000 tare da sharaɗin ka da su ƙara maimaita irin wannan laifi.
“Wannan yunƙuri namu yana nufin kare martabar Kano da al’adunta daga shigowar ɗabi’un da ba su dace ba, musamman a kafafen sada zumunta,” in ji Abba.
Alƙalin ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 17 ga watan Yuni, 2025, domin yanke hukunci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Abubakar Kilina ɗauri Gidan Yari Hukumar Tace Fina Finai Shigar mata
এছাড়াও পড়ুন:
An Jikkata Sojojin Sahayoniya 9 Ta Hanyar Take Su Da Mota
Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam.
Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba.
Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin ‘yan sahayoniyar da su ka jikkata sojoji ne.
Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; Wanda ya take sojojin ya iya gudu daga wurin, ba tare da an tsayar da shi ba.
Ita kuwa jaridar ‘ Yasrael Home” ta bayyana cewa; An baza ‘yan sanda a wurin da aka kai hari, domin gano inda maharin yake.
Kungiyoyin Falasdinawa sun yi maraba da wannan harin, tare da yin kira a ci gaba da gudanar da irinsa da yawa.
Kungiyar Hamas ta ce, dole a tsammaci wannan irin harin, bisa la’akari da laifukan da HKI take tafkawa a Gaza da yammacin kogin Jordan.
Kungiyar Jihadul-Islami kuwa cewa ta yi, hari irin wannan yana kara tabbatar da yadda al’ummar Falasdinu ta sha alwashin ci gaba da riko da kasarta da kuma kalubalantar ‘yan mamaya da dukkanin abinda su ka mallaka.
Shi kuwa kwamitin gwagwarmaya na Falasdinu ta yi kira ne ga dukkanin Falasdinawa da su yunkura domin fada da sojojin sahayoniya.
Ita kuwa kungiyar “Mujahidun-al-Falasdiniyya ta sa wa harin albarka tare da bayyana shi a matsayin babban sako ga ‘yan mamaya dake cewa martani akan kisan gillar da suke yi zai fadada.