Trump Ya Umarci A Bincika Lafiyar Ƙwaƙwalwar Tsohon Shugaban Ƙasa Biden Yayin Mulkinsa
Published: 5th, June 2025 GMT
Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan fitowar wani littafi mai taken Original Sin da ya zargi wani na kusa da Biden da ɓoye yadda jikinsa ya gaza yayin yaƙin neman zaɓen 2024, wanda daga ƙarshe ya janye. Wannan ya ƙara sanya tambayoyi kan ko an san da cutar sankarar da ya kamu da ita tun da wuri, musamman ganin yadda aka ce ta bazu zuwa ƙasusuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Dage Shari’ar Zargin Cin Hanci Da Ake Yi Wa Shugaban KANSIEC Na Kano Zuwa Nuwamba
Masu ƙarar sun bayyana cewa an ce an bai wa kamfanin kuɗin ne domin samo kuɗin hannu don biyan ma’aikatan wucin gadi da aka ɗauka a zaɓukan ƙananan hukumomi na 2024. Daga bisani kuma, an ce an dawo da kuɗin a matsayin tsaba zuwa hukumar.
Lauyan ICPC, Barr. Enosa Omoghibo, ya shaida wa kotu cewa an shirya fara gurfanar da waɗanda ake zargi ne, amma “ba su halarci kotu ba.”
Sai dai Lauyan waɗanda ake ƙarar, M.A. Magaji (SAN), ya ce abokan hulɗarsa ba su samu takardun shigar da ƙara kotu ba. Ya ƙara da cewa isar da takardu abu ne mai muhimmanci kafin kotu ta iya ci gaba da shari’a.
Daga nan ne kotu ta dage ci gaba da shari’ar zuwa 24 ga Nuwamba, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp