Adadin ‘Yan Jaridar Falasdinu Da Suka Yi Shahada Sun Karu Zuwa 226 Tun Bayan Fara Kisan Kare Dangi A Gaza
Published: 6th, June 2025 GMT
Adadin ‘yan jarida wadanda suka yi shahada a Gaza ya karu zuwa 226 tun bayan fara kisan kare dangi kan yankin
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar a yau Juma’a cewa: Adadin ‘yan jaridun da suka yi shahada ya karu zuwa 226, bayan sanar da shahadar dan jarida Ahmed Qaljah.
Ofishin ya bayyana cewa: Yawan ‘yan jaridan da suka yi shahada ya karu zuwa 226 tun farkon yakin kisan kare dangi kan zirin Gaza, bayan sanar da shahadar daya daga cikin ‘yan jaridan Falasdinawa: Ahmed Qaljah, wanda ya yi aiki a matsayin mai daukar hoto na gidan talabijin na Al-Arabiya.
Ofishin ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai hare-haren wuce gona da iri da kashe-kashen kare dang ikan al’ummar Falasdinu da kuma kashe ‘yan jaridar Falasdinawa. Don haka ta jadada yin kira ga kungiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa, kungiyar ‘yan jarida ta Larabawa, da dukkanin kungiyoyin ‘yan jaridu a duniya da su yi Allah wadai da wadannan laifuffuka na yau da kullun kan ‘yan jarida a Falasdinu wadanda suka kasance kwararrun kafafen yada labarai a zirin Gaza.
Ofishin yada labarai na gwamnati ya dora laifukan kisan kare dangin kan gwamnatin mamayar Isra’ila, gwamnatin Amurka, da kasashen da ke da wasu kasashen Turai musamman kasashen Birtaniya, Jamus, da Faransa, da alhakin aikata wadannan munanan laifuka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA