HausaTv:
2025-09-17@22:08:52 GMT

Ghana Ta Kawo Karshen Goyon Bayan Da Take Bawa Kungiyar Polisario

Published: 8th, June 2025 GMT

Kasar Ghana ta kawo karshen goyon bayan da take bawa kungiyar Polisario, sannan ta dawo tana goyon bayan kasar Morocco a kan wannan rikicin.

Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa, an kafa kungiyar Polisario ne a shekara 1979. Sannan rikicin Polisario yana komawa zuwa shekara 1975 a lokacinda turawan Espania yan mulkin mallaka suka fice daga yankin sai suka hadda fada tsakanin Polisario da kasashen Morocco da kuma Mauritania.

Kungiyar dai tana samun goyon bayan kasashe kimani 80 a duniya, amma kuma a hankali-a hankali tana rasa goyon bayan da take da samu a duniya, na karshensu it ace kasar Ghana.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: goyon bayan

এছাড়াও পড়ুন:

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

A bayan bayan nan, an aiwatar da jerin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka karkashin jagorancin shugabanninsu, inda aka samu kyawawan sakamakon da ya kyautata alakarsu ta tattalin arziki da cinikayya. Wannan ya nuna shawarar da a kullum Sin ke bayarwa cewa, tattaunawa ita ce mafita ga dukkan rikice-rikice, maimakon amfani da karfi.

Kasar Sin ta sha nanata cewa, babu mai samun nasara a yakin cinikayya ko haraji. Mun ga yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki da karuwar rashin aikin yi da faduwar darajar hannayen jari a Amurka, a lokacin da ta kaddamar da yakin haraji, wanda ya nuna cewa, maimakon cimma abun da take fata na samun fifiko, asara aka samu da lalacewar muradun kamfanoni da ’yan kasuwar kasar.

Kowace kasa tana da cikakken iko da ’yancin zabar manufofi da matakan da ya dace da ita. Da Sin ta tsaya kai da fata cewa ba za ta ba da kai a yakin haraji da Amurka ta tayar ba, hakan ya sa Amurka yin karatun ta nutsu, kuma ta tuntubi bangaren Sin domin tattaunawa.

Wadannan misalai sun nuna mana cewa, akwai hanyoyi masu sauki da inganci na samun maslaha, kuma shawarwarin da Sin take gabatarwa, su ne suka dace da yanayin duniya a yanzu. Ba dole sai kowa ya samu abun da yake so ba, amma hawa teburin sulhu da tuntubar juna tana taka muhimmiyar rawa wajen warware sabani, da lalubo inda kowane bangare zai iya saki, domin a samu mafitar da za ta karbu ga kowa. Kuma irin wannan din, shi ne burin sabuwar Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar a baya bayan nan. Duniya ba ta bukatar mayar da hannu agogo baya ta hanyar tayar da rikice-rikice da danniya da nuna fin karfi, zamani ya sauya kuma dole salon tafiyar da harkoki ya sauya, domin dacewa da yanayin da ake ciki.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces