HOTUNA: Yadda ambaliya ta raba mutane da muhallansu a Mokwa
Published: 5th, June 2025 GMT
Wasu daga cikin mazauna yankin Mokwa da ambaliyar ruwa ta lalata wa gidaje a Jihar Neja, yanzu na zaune a sansanin ’yan gudun hijira.
Ambaliyar, wadda ta kashe sama da mutum 100, ta jawo asarar dukiya da lalacewar gidaje da dama a yankin.
Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ambaliyar Mokwa: An gano gawar yara 7, jama’a na neman agajiAminiya ta kai ziyara sansanin a ranar Talata, inda ta ɗauki wasu hotuna da ke nuna halin da waɗanda abin ya shafa ke ciki da yadda suke rayuwa a sabon wajen da suka koma.
Ga hotunan a ƙasa:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Mokwa
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 8 A Jihar Filato
Wani ganau mai suna Kespan Iliya wanda shi ma mazaunin unguwar ne ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan unguwar na cikin barci lokacin da ‘yan bindigar suka iso cikin shigar kwamandoji, inda suka rika harbe-harbe kan mazauna unguwar.
LEADERSHIP ta fahimci cewa, sama da gidaje 96 ne kuma aka kone a Gyenbwas, al’ummar gundumar Langai ta karamar hukumar Mangu a yayin harin.
Kokarin jin ta bakin jami’im yada labarai na rundunar ‘Operation Save Haven (OPSH)’, Manjo Samson Zhakom ya ci tura domin wayarsa a kashe take a lokacin rubuta wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp