Ribadu Ya Kara Jaddada Gargadinsa Kan Biyan Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane
Published: 6th, June 2025 GMT
Wani rahoton tsaro da hukumar Kididdiga (NBS) ta fitar a watan Disamban 2024, ta ce, yawan kudin fansa da jama’an Nijeriya suka biya ya zarce naira tiriliyan 2.23 ga masu garkuwa da mutane daga Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.
A cewar rahoton na CESPS, kusan kashi 65 cikin 100 na magidanta da suka fuskanci matsalar sace-sacen jama’a sun biya matsakaitan kudin fansa na naira miliyan 2.
An fitar da rahoton ne kwana guda bayan rahoton hukumar kare kakkin Dan’adam na Nijeriya na shekarar 2024, ya nuna cewa akalla mutane 526 ne aka kashe a wasu munanan hare-hare tare da yin garkuwa da wasu 949 a wasu sassan kasar.
Duk da masana sun sha nusar da jama’a illar biyan kudaden fansa ga ‘yan fashin daji, mutane ko iyalai suna ganin biyan kudin shi ne mafita a garesu a duk lokacin da aka sace musu wani nasu, lamarin da ke kara nuna sakacin jami’an tsaro, a cewar mutane da dama in ba su biya kudin fansar ba suna iya rasa dan uwan nasu da aka sace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
HKI Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kudancin Kasar Lebanon
A dai-dai lokacinda jiragen yakin HKI suke ci gaba da kai hare-hare kan mutanen kudancin Lebanon sannan suka ci gaba da keta hurumin yarjeniyar da aka cimma da kungiyar Hizbullah, tana kashe mutanen kasar Lebanon. A wani bangare kuma Sojojin UNIFEL suna fuskantar turjiya daga mutanen kudancin kasar ta Lebanon.
Jaridar Arba News ta kasar Saudia ta bayyana cewa mutane a yankin sun hana sojojin UNIFEL shiga wasu unguwanni a yankin don gudanar da bincike a cikin gidajen mutane.
Labaran da suke fitowa daga irin wadannan yankuna sun nuna cewa muatne sun hana sojojin nUnufel shiga wasu unguwanni, sai sun kawo sojojin kasar Lebanon .
Sojojin sun dage saisun shiga amma mutane sun hansu shiga a sannane suka fara amfani da teas gas ko iska mai sa hawaye don tarwatsa su. Wannan bai yi amfani ba.
Gwamnatin kasar Lebanon ta bukaci a tsawaita lokacin wanzuwar sojojin UNIFEL a kudancin Lebanon amma ta bayyana a fili sojojin suna aiki wa HKI da Amurka ne.