Darajar Hajojin Da Aka Yi Jigilarsu a Kasuwar Sin Daga Watan Janairu Zuwa Na Afrilu Ta Karu Da 5.6%
Published: 3rd, June 2025 GMT
Yau Talata, kungiyar masu jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta gabatar da alkaluman watanni 4 na farko na bana, wadanda suka nuna cewa, a watan Afrilu, sha’anin jigilar kayayyaki ya bayyana inganci da boyayyen karfi, kuma duk da kalubaloli da matsin lamba daga ketare da aka fuskanta, ya tafi yadda ya kamata tare da samun bunkasuwa.
Kazalika, yawan hajojin da aka yi jigila yana cikin wani yanayi mai dorewa, bisa la’akari da yadda jigilar kayayyaki ta amfani da layin dogo da hanyoyin mota ke tafiya yadda ya kamata, kana ana samun saurin bunkasuwar jigilar kayayyaki da ta hada mabambantan hanyoyi. Alkaluman sun kuma nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Afrilu, yawan hajojin da aka yi jigila ta hanyar layin dogo ya karu da kashi 3.6 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokacin a bara, adadin na hanyoyin mota ya karu da kashi 5 cikin kashi 100, kana yawan kwantanonin da aka yi jigilar su ta amfani da jirgin kasa da na ruwa tare, ya wuce miliyan 5.38, wanda ya karu da kashi 19.1 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokacin a bara. Nauyin yawan sakwanni da aka yi jigila ya kai fiye da ton miliyan 3, adadin ya karu da kashi 13 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokacin bara. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: jigilar kayayyaki ya karu da kashi
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA