Ministan Tsaro Ya Yi Gargadin Sake Dawowar Boko Haram Na Barazana Ga Nijeriya
Published: 6th, June 2025 GMT
“Idan za ku yi adalci a gare mu, a cikin makonni biyu da suka gabata, za ku ga cewa sojojin suna samun nasara wajen karya lagon ‘yan ta’adda, inda suka kashe su tare da tarwatsa sassaninsu,” in ji ministan.
A karshen makon da ya gabata, wadanda ake zargi ‘yan ta’adda na Boko Haram sun dasa na’urorin fashewa a Unguwar Guzamala na Jihar Borno, inda suka kashe mutane tara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara
A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara.
A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da fasinjoji ta faɗa cikin gadar da ta ruguje. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SRC Isah Aliyu, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar.
Kwamandan FRSC na jihar, CC Aliyu Magaji, wanda ya ziyarci wurin hatsarin, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa da asarar rayukan, inda mafi yawansu mata ne. Ya ce hatsarin ya biyo bayan nauyin da aka ɗora wa motar fiye da ƙima da kuma tafiya da daddare.
Hukumar ta gode wa mazauna yankin da suka gaggauta taimakawa wajen ceto wasu daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su. Kwamanda Aliyu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Zamfara da al’ummar Gummi, tare da yin kira ga direbobi su rika bin ƙa’idojin hanya da kuma guje wa tuƙa mota da dare domin kare rayuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp