Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu
Published: 7th, June 2025 GMT
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta sallami kocinta Ange Postecoglu ƙasa da wata daya bayan ya lashe kofin Uefa Europa League na bana, Ange wanda ya zo Tottenham daga Celtic ya shafe shekaru biyu ya na jan ragamar kungiyar.
Shugaban Tottenham Levy ne ya bayyana wannan mataki na sallamar Ange bayan wani taro da mahukuntan ƙungiyar suka yi a ranar Juma’a, wanda ya ce hakan shi ne mafita ga ɓangarensu da kuma ɓangaren kocin wanda ya jagoranci wasanni 101 a matsayin koci.
A zahiri, alaƙar babban kocin da tawagarsa ta zama ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa kocin mai shekaru 59 ya ci gaba da zama, amma kwanaki 16 kacal bayan nasarar lashe kofin Yefa Europa League a Bilbao, an kori Postecoglou shekaru biyu kacal da zuwanshi Landan.
Tottenham ta samu nasarar lashe kofin Europa League bayan da ta doke abokiyar karawarta Manchester United a wasan ƙarshe da aka buga a filin wasa na San Mames da ke birnin Bilbao, kafin zuwa Ange kungiyar dake gabascin Landan ta shafe shekaru fiye da 20 ba tare da lashe wani kofi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.
Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.
Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da AmurkaA cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.
“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.
Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.
“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.
Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.
“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.