Lambar “-1.5” Gargadi Ce Da Al’ummar Duniya Ke Yi Ga Azzaluma
Published: 6th, June 2025 GMT
“Al’ummar kasa da kasa da yawa sun sauya ra’ayinsu mai kyau game da Amurka zuwa mummunan ra’ayi, yayin da yawan masu nuna kauna ga kasar Sin ya karu.” Wani bincike da kamfanin bincike na Morning Consult na Amurka ya fitar kwanan nan ya nuna cewa, har zuwa karshen watan Mayu, yawan al’ummar duniya dake nuna kauna ga Amurka ya ragu zuwa -1.
Wannan sakamakon ba wani abu ne da ya faru ba zato ba tsammani ba. Tun daga farkon bana, matakin kakaba haraji da Amurka ta dauka ba bisa ka’ida ba ya kawo jerin munanan tasirori, wanda ya haifar da illa ga tattalin arzikin duniya, kuma Amurka ita kanta ta sha wahala daga irin wannan matakin.
Su wane ne masu lalata cinikin duniya? Su wane ne masu kare ciniki cikin ’yanci? Jama’ar duniya sun sani a bayyane.
Yanzu dai kasashe da yawa sun gane cewa, manufar “Amurka gaba da kome” ba za ta haifar da kome ba sai rikice-rikice kawai, kuma mika wuya ga matakin zaluncin haraji zai haifar da karin matsawa kawai. Sai dai ta hanyar hadin kai, dogaro da kai da nemo cimma nasara tare ne kawai za su iya kare hakkokinsu da muradunsu da ma samun ci gaba tare. Wannan binciken jin ra’ayin jama’a gargadi ne da duniya ya yi ga Amurka, wato idan ta ci gaba da shagala da ra’ayin samun riba kan asarar wani bangare, za ta rasa dukkan kasashe masu kawance da ita. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau 17 ga wata, inda aka bayyana cewa, tun daga fara aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 na raya kasa, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, karfin kamfanoni mallakar gwamnati ya kara karuwa, kuma jimillar kadarorinsu ta wuce yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6.
Darektan kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Zhang Yuzhuo ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 har zuwa yanzu, jimillar kadarorin kamfanoni mallakar gwamnati ta karu daga kasa da yuan tiriliyan 70, kwatankwacin dalar Amurka kimanin tiriliyan 10, zuwa sama da yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6, yayin da jimillar ribar da suka samu ta karu daga yuan tiriliyan 1.9, kwatankwacin sama da dalar Amurka biliyan 267, zuwa yuan tiriliyan 2.6, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 365. Matsakaicin karuwar jimlolin biyu a kowace shekara kuwa ya kai kashi 7.3 cikin dari da kashi 8.3 cikin dari bi da bi.
Bugu da kari, tun daga aka fara aiwatar da shirin, kamfanoni mallakar gwamnati sun biya kudin harajin da yawansu ya zarce yuan tiriliyan 10, kwatankwacin fiye da dalar Amurka triliyan 1.4, kuma darajar yawan hannun jarin da suka mikawa asusun inshorar zaman al’umma ta kai yuan tiriliyan 1.2, kwatankwacin fiye da dalar Amurka biliyan 168.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp