Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna tace shirin Bus Rapid Transit BRT da ake shirin kaddamarwa zai taimaka matuka wajen rage kudaden sufuri ga mazauna jihar, da zarar an fara aiwatar da shi.

 

Daraktan Hukumar, Injiniya Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kada Hive da ke Kaduna.

 

An shirya taron ne domin wayar da kan jama’a game da shirin BRT, sannan matakan da aka dauka ya zuwa yanzu.

 

Taron an gudanar da shi ne domin sauraron ra’ayoyin al’umma kan yadda za a aiwatar da shi cikin nasara.

 

Injiniya Inuwa ya bayyana cewa tsarin BRT zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa da kara tsaro da aminci, da kuma inganta rayuwar al’umma baki daya a Jihar Kaduna.

 

Ya tuna cewa kimanin watanni biyu da suka gabata ne Gwamna Uba Sani ya kaddamar da sama da motoci 100 masu amfani da iskar gas na CNG, wadanda za su rika zirga-zirga a cikin Birnin Kaduna, Zariya da Kafanchan, a wani bangare na kokarin gyara tsarin sufuri a fadin jihar.

 

Ya bukaci mahalarta taron su yada ilimin da suka samu zuwa cikin al’ummominsu domin kara fahimta da goyon bayan jama’a don nasarar wannan shiri.

 

A nasa bangaren, Ted Regino, shugaban Rebel Artic Joint Venture, wanda ke sa ido kan kwangilolin aikin, ya ce kamfaninsa ne ke lura da yadda ake gudanar da aikin.

 

Ya tabbatar da cewa za a kammala aikin BRT kafin shekarar 2027, tare da karin bayani cewa kamfaninsu ya taba aiwatar da manyan ayyuka a kasa da kasa, kuma hakan zai maimaitu a Jihar Kaduna.

 

A nata jawabin, Shugabar Jam’iyyar Matan Arewa, Hajiya Rabi Saulawa, ta yaba da wannan shiri, tana mai cewa zai rage wa mata wahalhalun sufuri, musamman wadanda ke yawan zirga-zirga zuwa asibitoci, kasuwanni, wuraren aiki da makarantu.

 

Wasu daga cikin mahalarta sun jaddada bukatar kulawa da kiyaye motocin, tabbatar da dorewar shirin, da kuma kawo karshen matsalar sayar da tikiti ba bisa ka’ida ba.

 

Taron ya samu halartar wakilai daga sashen sufuri, shugabannin addinai da na gargajiya, ’yan jarida da sauransu.

 

COV: Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Sabon Tsarin Sufuri Na BRT Zai Rage

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Damƙe Ɗan Fashi, Sun Kwato Makamai A Kaduna Da Filato

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Wakilai Ta Fara Binciken Yadda Aka Raba Naira Tiriliyan 1.12 Kan Shirin Lamuni Ga Manoma Da Masana’antu
  • Daga Taklimakan Zuwa Sahara: Karin Abubuwan Al’ajabi Na Faruwa Bisa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Yaki Da Kwararar Hamada
  • Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran
  • Sabon Shirin Gwamnatin Katsina: Za A Fara Sauya Tunanin Tubabbun ‘Yan Bindiga
  • Sojoji Sun Damƙe Ɗan Fashi, Sun Kwato Makamai A Kaduna Da Filato
  • Shugabannin Duniya Za Su Gudanar Da Taron Sanya Hannun Jarin Bunƙasa Ƙudurorin Muradun Ƙarni A Sifaniya
  • Sojojin Kasar Iran Sun Ce Bazasu Dakatar Da Yaki ba Har Zuwa Samun Nasara A kan HKI
  • APCn Kaduna Ta Mara Wa Tinubu, Uba Sani Da Kakakin Majalisa Abbas Baya Don Wa’adi Na Biyu
  • NAF Na Shirin Siyo Jiragen Yaki Masu Saukar Ungulu Daga Amurka
  • Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Bayyana Sabon Salon Mayar Da Martani Kan Isra’ila