Hako Man Fetur: Jihar Neja Ta Nemi Hadin Gwiwar Kamfanin Dangote
Published: 8th, June 2025 GMT
Wani rahoto na binciken yanayin kasa na shekarar 2023 ya gano bututun mai guda 17 da za aiya cin kasuwa da shi a Jihar Neja, tare da kiyasin da aka yi na zai hako iskar gas har ta tsawon shekara 70.
Basin na Bida, wanda ya ratsa sassan jihohin Neja da Kwara, an gano shi a matsayin yankin da ke kwararo albarkatun mai mai cike da fa’ida.
Wakilin rukunin Dangote, Mista Hashem Ahmed, ya ce kamfanin yana zuba jari sosai a Jihar Neja, ya kara da cewa a shirye yake ya hada gwiwa da jihar domin ba ta damar bunkasa abubuwan da ta ke da su.
“Kamfanin Shinkafa na Dangote da ke Wushishi idan an kammala shi zai inganta noman shinkafar cikin gida da kuma rage asarar da ake samu bayan girbi, muna kuma aiki kafada da kafada da ofishin gwamna kan shirin samar da abinci na Neja, shirin noma da ke taka muhimmiyar rawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara
Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna
Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya
Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar Katsina.
Shima da yake jawabi shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya yi alkawarin cigaba da wayar da kan al’umma akan wannan cuta ta shan Inna da sauran cututtuka masu kashe yara a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
Wadanda suka shaida wannan bikin ranar ‘Polio’ ta duniya sun hada da hukumar lafiya ta WHO da kuma masu lalurar cutar shan Inna da wakilan asusun UNICEF da matan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
ShareTweetSendShare MASU ALAKA