Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe
Published: 7th, June 2025 GMT
A yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, a duk irin kalubalen da za a iya samu daga waje, masana’antun kasar Sin za su ci gaba da zama ababen nema a duniya, kuma kasuwannin kasar za su kasance a ko yaushe masu jan hankali wajen zuba jarin waje.
An ba da rahoton cewa, a yanayin tangardar da tattalin arzikin kasa da kasa ke fuskanta, huldar kasuwanci da tattalin arzikin kasar Sin da sauran kasashen duniya na nan daram ko gezau.
Daga watan Janairu zuwa Afrilu, yawan kayayyakin da ake jigilarsu ta tashar jiragen ruwa na kasar Sin ya kai tan biliyan 5.755, wanda ya karu da kashi 3.7 bisa dari a mizanin shekara-shekara, kuma yawan kwantenoni masu fadin kafa 20 da aka yi jigilarsu ta tashar jiragen ruwan dakon kaya na kasar Sin ya zarce miliyan 110, wanda ya karu da kaso 7.9 bisa dari a mizanin kowace shekara.
Bugu da kari, jami’in ya ce, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da nuna bajintar kuzarinsa, kuma yana kara samun karbuwa a harkokin kasuwanci cikin karfi. Inda hakan ke cikakken nuna cewa, a duk wani kalubale da za a iya samu daga waje, masana’antun kasar Sin za su ci gaba da zama ababen nema a duniya, kuma kasuwannin kasar ta Sin za su kasance masu jan hankali wajen zuba jarin waje. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Aikin Zirga-Zirgar Jiragen Sama Ta Fasinja Ta Sin Ya Bunkasa Zuwa Sabon Matsayi
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ta kasar Sin ta fidda bayani a jiya Talata cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, yawan zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ya kai ton-kilomita biliyan 78.35, adadin da ya karu da kaso 11.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Kana, yawan zirga-zirgar fasinjoji ya kai miliyan 370, wanda ya karu da kaso 6 bisa dari. A sa’i daya kuma, yawan zirga-zirgar hajoji da kunshin kayayyaki ya kai ton miliyan 4 da dubu 784, wanda ya karu da kaso 14.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Cikin taron aiki da hukumar zirga-zirgar jigaren sama ta fasinja ta kira a jiyan, shugaban hukumar Song Zhiyong ya bayyana cewa, an gudanar da aikin tsaro yadda ya kamata, ganin aikin zirga-zirgar jiragen sama ya karu da kaso 5.6 bisa dari cikin rabin farkon bana, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.
Haka zalika, a rabin farkon na bana, tsawon lokacin zirga-zirgar jiragen sama na gama gari ya kai awoyi dubu 570, kana, yawan jiragen sama marasa matuki da jama’ar kasa suka yi rajista ya kai miliyan 2 da dubu 726. Lamarin da ya nuna cewa, harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta gama gari, da tattalin arzikin jiragen saman dake zirga-zirga kusa da doron kasa, suna bunkasuwa bisa tsari. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp