Sabon injin jirage masu saukar Ungulu kirar kasar Sin samfuin AES100, ya samu shaidar amincewar inganci da damar sayar da shi a kasuwanni, matakin da ya kafa harsashin bunkasa samar da kayayyakin bukata a fannin kirar ababen hawa masu tashi kurkusa da kasa.

 

Kungiyar makera injuna ta kasar Sin ce ta sanar da wannan ci gaba a yau Alhamis, inda ta ce sabon samfurin injin shi ne irinsa na farko da aka kera a Sin bisa fasahohin kasar na kashin kai, wanda ke da fasahar karfin “kilowatt 1,000”, ya kuma yi nasarar cika darajar karko ta kasa da kasa.

(Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya Ya Jaddada Goyon Bayan Kasarsa Ga Iran

Yarima mai jiran gadon Saudiyya ya tabbatarwa shugaban kasar Iran cewa: Saudiyya tana goyon bayan Iran

Yariman mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya tabbatar da hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Asabar, yana mai jaddada cewa: Masarautar Saudiyya da daukacin al’ummar musulmin duniya sun hadu a kan goyon bayan Iran.

Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya ya ce: Dukkanin al’ummomin kasashen musulmi a yau suna da hadin kai da jaddada goyon bayansu ga Iran, kuma yana iyaka kokarinsa a fagen diflomasiyya da matsin lamba na kasa da kasa don dakatar da wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan Iran.

Bin Salman ya yi Allah wadai da hare-haren rashin adalci da ‘yan sahayoniyya suke kaiwa Iran.

Ya kuma bayyana jimaminsa tare da jajantawa al’ummar kasar Iran dangane da wadannan hare-hare da suka rutsa da su, yana mai jaddada cewa: Saudiyya tana da tabbataccen matsayi kan tsayawa tare da ‘yar uwarta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma duniyar musulmi a yau ta hade kan muryar daya wajen goyon bayan Iran.

Ya ci gaba da cewa: “Mun yi imanin cewa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na neman ta hanyar kara kunna wutar rikici ta janyo Amurka a cikin tsakiyar rikici, amma suna da yakinin cewa martanin Iran a kan ma’aunin daidaito da matakan hankali zai dakile wannan  yunƙurin makirci.”

Bin Salman ya kuma jaddada cewa: Kasarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da duk wani tallafi da ya dace ga ‘yan uwanta Iran.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masu Karanta Adabin Shafin Intanet Na Sin Sun Kai Miliyan 575
  • Masu Garkuwa Da Mutane Sun Dira Jihar Kogi, Sun Sace Wani Basarake
  • Sin Ta Fatattaki Laifukan Zamba Ta Shafin Intanet 294,000 A Bara
  • PLA Reshen Kudancin Kasar Ta Yi Sintiri Na Hadin Gwiwa A Tekun Kudancin Sin
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Ba’a Rufe Kofar Diblomasiyya Ba, Matukar HKI Ta Dakatar Da Kaiwa Kasar HKI
  • Wang Yi Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Isra’ila
  • NAF Na Shirin Siyo Jiragen Yaki Masu Saukar Ungulu Daga Amurka
  • Martanin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Ta’addancin ‘Yan Sahayoniyya ya Shiga Rana Ta Biyu
  • Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya Ya Jaddada Goyon Bayan Kasarsa Ga Iran
  • An Yi Zanga-zangar Nuna Goyon Baya Ga Kin Amincewa Da Bakin Haure A Amurka