Matar aure ta banka wa mijinta wuta
Published: 24th, February 2025 GMT
An gurfanar da wata matar aure a kotu kan zargin ta da cinna wa mijinta wuta a Jihar Kano.
Ana zargin matar ta watsa wa mijin nata fetur sannan ta cinna masa wuta ne saboda ya shiga dakin sabuwar amaryarsa, suna tattaunawa da ita.
Shaidu sun bayyana cewa wadda ake zargin ta yi aika-aikan ne bayan ta nemi mijin nata ya fito daga dakin amaryar tasa amma ya ƙi amincewa.
Magidancin ya samu munanan kuna a sakamakon wutar da matar tasa ta yi masa.
Lauyar Gwamantin Jihar Kano, Saima Garba, ta karanta wa matar takardar tuhumar aikata kisa da ake mata, amma ta musa.
Daga nan alƙalin kotun Majistare mai Lamba 25, Halima Wali, ta ba da umarnin tsare matar a gidan yari sannan ta ɗage sauraron shari’ar da makonni biyu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Kammala Gyaran Makarantu Sama Da 1,200 A Kananan Hukumomi 44
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala gyaran makarantu fiye da 1,200 a kananan hukumomi 44 na jihar a wani yunkuri na farfado da harkar ilimi.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin taron bitar yini guda kan kara kaimi a tsarin duba ingancin karatu, da aka gudanar a dakin taro na Cibiyar Kula da Ilimin Al’umma (CERC).
Ya ce banda gyaran manyan makarantu, gwamnatin ta ware Naira miliyan 484 domin gudanar da karin ayyukan gyare-gyare a gundumomi 484, inda kansilolin mazabu ke kula da gudanarwar ayyukan.
“A karo na farko a tarihin Kano ake aiwatar da manyan ayyukan ilimi a wannan mataki. Mun riga mun gyara makarantu sama da 1,200 kuma an fara ayyuka a matakin gundumomi.” In ji Dr. Makoda.
Kwamishinan ya kara da cewa wannan ci gaba yana cikin matakan aiwatar da dokar ta-baci da aka ayyana kan harkar ilimi a watan Mayun 2024, domin dawo da martabar fannin.
Ya ce gwamnatin ta kuma amince da Naira biliyan 3 domin gyaran makarantun kwana 13 na ’yan mata da gwamnatin da ta shude ta rufe.
Dr. Makoda ya bayyana cewa Kano na da fiye da makarantu 30,000, adadi mafi yawa a duk fadin Najeriya, kuma gwamnati na da niyyar ganin kowanne yaro ya samu ingantaccen ilimi cikin daidaito.
Taron ya horar da daraktoci, shugabannin makarantu da jami’an sa-ido, inda kwararru irin su Farfesa Ahmed Ilyasu da Bashir Sule suka gabatar da jawabai kan hanyoyin tantance darussa da dabarun inganta ilimi.
Daga Khadijah Aliyu