Kocin Inter Milan Simone Inzaghi Ya Bar Kungiyar Kwanaki Biyu Bayan Rashin Nasara A Hannun PSG
Published: 4th, June 2025 GMT
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”.
Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro, sau biyu ya jagoranci Inter zuwa wasan karshe na gasar zakarun Turai amma Manchester City ta doke su da ci 1-0 a 2022-23 sannan suka sha kashi a hannun PSG da ci 5-0 a ranar Asabar din da ta gabata.
Sun kuma kasa cin kofin Seria A na 2024-25 bayan da Napoli ta basu maki daya kacal akan teburi, tafiyar Inzaghi na zuwa ne gabanin halartar Inter a gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa na Fifa da aka fadada, wanda zai gudana a Amurka tsakanin 14 ga watan Yuni zuwa 13 ga Yuli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.
Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.
A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.
Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp