Gwamnatin Kasar Chadi Ta Maida Martani Kan Dokar Hana Yan Kasar Shiga Amurka
Published: 6th, June 2025 GMT
Shugaban kasar Chadi Muhammad Deby ya maida martani ga shugaban kasar Amurka kan hana yan kasar Chadi shiga kasar Amurka da hana a bawa Amurkawa visar shiga kasar.
Jaridar PREMIUM TIMES ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban kasar Amurka a ranar Laraban da ta gaba ne ya sanya hannu a kan dokoki wadanda suka hana yan kasashe 12 shiga kasar Amurka sannan wasu 7 kuma za’a basu Visa shigar kasar tare da sharudda.
A jiya Alhamis ne shugaban Deby ya maida martani, da haka Amurkawa shiga kasarsa. Dokar dai ta hana kasashen Afirka guda 6 shiga kasar Amurka kuma sun hada da Chadin da kuma Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia da kuma Sudan.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Amurka shiga kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.
Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.
Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.
A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.
“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.
Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.
Tinubu ya kuma yaba wa masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.
Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.
Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.
Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.
Daga Bello Wakili