Matawalle ya yi wa Gwamna Lawal da wasu tayin shiga APC
Published: 8th, June 2025 GMT
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya buƙaci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Matawalle ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, a garinsu Maradun, yayin da dubban magoya bayansa suka kai ziyarar gaisuwar Sallah.
Sallah: Gwamnatin Sakkwato ta bai wa kowane Alhaji kyautar N450,000 Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na AjaokutaMatawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya ce APC jam’iyya ce ta mutanen kirki da masu kishin ƙasa.
Ya ce maimakon a ci gaba da takun-saka tsakanin gwamnati da ’yan adawa, zai fi kyau Gwamna Dauda ya fito fili ya rungumi jam’iyyar da ke da madafun iko domin ci gaban jihar da ƙasar gaba ɗaya.
“Idan Gwamna Dauda na da niyyar kawo ci gaba musamman a fannin tsaro da zaman lafiya, babu laifi ya zo ya haɗu da sauran ’yan kwamitin ci gaba a APC,” in ji Matawalle.
Matawalle, ya jaddada cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙari wajen samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa, kuma yana buƙatar goyon bayan gwamnonin jihohi da sauran shugabanni don cimma nasara.
A baya-bayan nan, wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa da dama sun sauya sheƙa zuwa APC.
Sun bayyana cewa suna son su haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen samun mafita ga matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Wannan na ƙara wa APC ƙarfi a jihohi da dama, ciki har da Zamfara.
Kiran da Matawalle ya yi wa Gwamna Dauda Lawal da wasu shugabannin adawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke ƙara karɓar sabbin mambobi daga jam’iyyun adawa, a wani yunƙuri na ƙarfafa tsarin mulki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamna Lawal matawalle Sauya Sheƙa Tsaro Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
Wani gidan shan kofi a birnin Dubai ya fara sayar da kofi guda na haɗaɗɗen kofi a kan kusan Dala 1,000, wato kimanin Naira miliyan 1.5, wanda da haka ya zama mafi tsada a duniya.
Gidan shan kofin mai suna Julith Café — da ke cikin unguwar masana’antu da ya zama sabuwar cibiyar masu son kofi, shi ne ya ƙaddamar da wannan sabon nau’in abin sha mai daraja.
Ana sa ran gidan shan kofi ɗin zai fara ba da wannan abin sha ga mutane kimanin 400 kacal, ciki har da wani ɗan adadi da aka tanadar wa dangin gidan sarautar Dubai.
Wani daga cikin masu mallakar gidan, Serkan Sagsoz, ya ce sun zaɓi Dubai ne saboda “birni ne da ya dace da irin jarin da ke nuna ƙawa da kuma salo.
“Mun ga Dubai a matsayin wuri mafi dacewa don wannan kasuwanci. Wannan birni ne da ke son abubuwan da suka bambanta,” in ji Sagsoz.
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangiKofin kofi ɗin, wanda ake sayarwa a kan Dirhami 3,600 (kimanin 980), an yi shi ne daga ’ya’yan kofi na musamman da ake kira Nido 7 Geisha ,daga ƙasar Panama — waɗanda aka saya a gasa ta duniya bayan tashin rububin mai tsanani tsakanin masu saye.
Kamfanin Julith Café ya ce ya biya kimanin Dirhami miliyan 2.2 (dala 600,000) don sayen kilo 20 na waɗannan ’ya’yan kofi, abin da ya kafa sabon tarihin farashi mafi tsada da aka taɓa sayen kofi a duniya.
Sagsoz ya bayyana cewa kofi ɗin yana da ƙamshi da ɗanɗano na musamman. “Yana da ƙamshin furanni farare irin na jasmine, ɗanɗanon lemo da bergamot, har da ɗanɗano irin na apricot da peach. Kamar zuma yake — laushi kuma mai daɗi sosai.”
A bara, wani gidan kofi mai suna Roasters ya kafa tarihin Guinness na kofin kofi mafi tsada a duniya a Dubai, inda ya sayar da shi a kan Dirhami 2,500, amma yanzu Julith Café ta karya wannan tarihin.
Wasu mazauna Dubai sun ce duk da abin mamaki ne, amma abin ba baƙo ba ne a garin da aka sani da abubuwan alfarma.
“Abin mamaki ne amma ai wannan Dubai ce,” in ji wata mazauniya mai suna Ines.
“Ai akwai masu kuɗi, wannan wani sabon abin alfahari ne kawai,” in ji wata mai suna Maeva.
Ana sa ran gidan shan kofi ɗin zai fara ba da wannan abin sha ga mutane kimanin 400 kacal, ciki har da wani ɗan adadi da aka tanadar wa dangin gidan sarautar Dubai.
Shin idan kuna da kudin za ku saya?