Aminiya:
2025-06-18@03:00:28 GMT

Ba zan yi musayar yawu da yara ba — Martanin Amaechi ga Wike

Published: 4th, June 2025 GMT

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana dalilin da ya sa ya naɗa Nyesom Wike a matsayin Shugaban Ma’aikata a lokacin da yake Gwamnan Jihar Ribas, maimakon Kwamishinan Kuɗi.

Amaechi, ya ce ya zaɓi Wike ne a matsayin Shugaban Ma’aikata domin ya samu damar sanya ido a kansa.

Tinubu ya gana da Fubara a Legas Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja

“Na so ya zama shugaban ma’aikata ne saboda na riƙa sanha ido a kansa.

“Ban ba shi kujerar kwamishinan kuɗi ba,” in ji Amaechi a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise da yammacin ranar Talata.

Wannan martanin ya biyo bayan kalaman Wike ne, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya, inda ya yi martani kan wata magana da Amaechi ya yi a bikin cikarsa shekaru 60 a duniya.

Ya ce: “Dukaninmu muna jin yunwa.”

Wike ya ce Amaechi yana yunwarsa a fili kan lallai sai ya zama wani abu a siyasar Najeriya.

Sai dai Amaechi ya musanta zargin Wike na cewa shi ne ya taimaka masa ya zama gwamna.

“Ubangiji, tsohon gwamna Peter Odili, kotuna, da kuma al’ummar Jihar Ribas ne suka sa na zama gwamna,” in ji shi.

“Ka tambaye shi yadda ya sa na zama gwamna. Ina faɗin haka ne saboda bana so na yi musayar yawu da yara.”

Amaechi ya ƙara sukar Wike, inda ya ce a yanzu ba ya ganin girman kowa har waɗanda suka taimake shi a rayuwa.

“Ka ga shi ya naɗa kansa shugaban ma’aikata. Ya naɗa kansa gwamna. Ya yi wa kansa minista. Ya kuma yi wa kansa shugaban ƙaramar hukuma,” in ji Amaechi.

Amaechi ya ce bai ga amfanin yin cacar baki da Wike a bainar jama’a ba, domin hakan bai dace da shi ba.

“Ina faɗin haka ne saboda bana so na shiga cece-kuce da yara,” ya maimaita.

Rigima tsakanin tsoffin abokan siyasar biyu na ci gaba da jawo hankalin jama’a, musamman duba da tarihin siyasarsu a Jihar Ribas.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: martani Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Dira Jihar Kogi, Sun Sace Mutane 1

Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas.

Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace.

Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje

Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an sace Ajayi ne tsakanin karfe 9 zuwa 10 na safe, inda ‘yansanda da ‘yan sa kai suka fara bincike a dazuzzukan yankin.

Akwai bayanin cewa wasu sassan jihar na fama da hare-haren ‘yan fashi a baya-bayan nan, inda wasu mutane suka mutu yayin da ake sace-sace. Duk da haka, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya tabbatar da cewa gwamnati na ɗaukar matakai don magance wannan matsala.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Fatattaki Laifukan Zamba Ta Shafin Intanet 294,000 A Bara
  • Masu Garkuwa Da Mutane Sun Dira Jihar Kogi, Sun Sace Mutane 1
  • Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe
  • Tinubu ya bayar da umarnin binciken hare-haren Benuwe
  • Tinubu ya bayar umarnin binciken hare-haren Benuwe
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Sojojin Isra’ila Sun Kashe Kananan Yara Masu Yawa A Iran
  • Rundunar Sojin Ruwa Ta Nijeriya Ta Lalata Haramtattun Matatun Mai 5 A Ribas
  • Kakakin Gwamnatin Iran Ta Ce daga Yau Lahadi Wuraren Fakewa A Bude Suke Sa’o’I 24 A Tehran
  • Martanin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Ta’addancin ‘Yan Sahayoniyya ya Shiga Rana Ta Biyu
  • Martanin sojojin Iran ga Isra’ila zai zama mafi muni idan aka ci gaba da kai hari (Pezeshkian)