Kotun ICC Ta Yi Tir Da Amurka Saboda Takunkuman Da Ta Dorawa Alkalan Kotun Don Hanata Aikinta Da Yenci
Published: 6th, June 2025 GMT
Kotun kasa da kasa ta ICC ta yi tir da gwamnatin kasar Amurka wacce ta kakabawa al-kalan kotun guda hudu saboda hannu da suke da shi wajen fidda sammacin kama fray ministan HKI Benyamin Natanyahu.
Kotun ta kara da cewa tana goyon bayan alkalanta kuma zata ci gaba da aikinta na tabbatar da adalci a duniya duk tare da abinda suke faskanta.
Takunkuman dai ya shafi wadannan alkalai su 4 kuma mata. Kuma sun hana ko wanne daga cikinsu, shiga kasar Amurka kuma idan suna da kadarori ko kudade gwamnatin Amurka ta kwace su.
A cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 ne dai kotun ta ICC wacce take zama a birnin Haque ta fidda sammacin kama Firay ministan HKI Benyamin Natanyahu da kuma tsohon ministan yakin kasar Yoav Galant saboda zargin aikata laifukan yaki a Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp