Sabon Shugaban Koriya Ta Kudu Ya Yi Alkawarin Sulhu Da Takwaransa Na Arewa
Published: 4th, June 2025 GMT
“Za mu warkar da raunukan rarrabuwar kawuna da yaki da kuma kafa makomar zaman lafiya da wadata,” in ji shi. “Komai runtsi, zaman lafiya ya fi yaki.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Amurka: An gabatar da daftarin kudirin sake duba alaka da Afirka ta kudu
‘Yan majalisar dokokin Amurka sun gabatar da wani kudirin doka da ke ba da shawarar sake duba alakar Amurka da Afirka ta Kudu da kuma kakaba takunkumi a kan wasu jami’ai da suka ki amincewa da manufofin Amurka na ketare.
Kwamitin harkokin wajen Amurka ya kada kuri’a don aikewa da daftarin kudiri a kan yin nazarin dangantakar Amurka da Afirka ta Kudu” zuwa ga babban zauren majalisar wakilai, inda za a kada kuri’a a kansa.
Wannan matakin na bukatar amincewa daga majalisun wakilai da na dattawa kafin ya zama doka, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
‘Yar majalisar wakilai Ronny Jackson ce ta gabatar da kudirin dokar a watan Afrilun da ya gabata. Tana zargin Afirka ta Kudu da zagon kasa ga muradun Amurka ta hanyar kulla alaka ta kut da kut da Rasha da China, da kuma nuna adawa ga Isra’ila, gami da kuma gurfanar da ita a gaban kotun kasa da kasa kan batun kisan gilla a a kan al’ummar Palasdinu.
Kudirin ya ba da shawarar yin cikakken nazari kan alakar kasashen biyu da kuma bayyana jami’an gwamnatin Afirka ta Kudu da shugabannin jam’iyyar ANC wadanda suka cancanci a kakaba musu takunkumi.