Jirgin Ruwa “Madeleine” Dake Son Karya Takunkumin Gaza Yana Ci Gaba Da Tafiya
Published: 8th, June 2025 GMT
Jirgin ruwan na “Madeleine” shi ne na 36 a cikin jerin jiragen ruwan ‘yanci da suke son karya takunkumin da aka kakabawa yankin Gaza tun 2007.
A cikin wannan jirgin ruwan da akwai ‘yan gwgawarmaya masu rajin kare hakkin bil’adama su 12 da su ka fito daga kasashe daban-daban, yana kuma dauke da kayan agaji na abinci da magani.
Jirgin ruwan ya samo sunansa ne daga wata Bafalasdiniya mai suna; Madeleine Kulaib, wacce ita ce macen farko ta Falasdinu da ta kware a sana’ar kama kifi bayan da mahaifinta ya yi shahada a yayin yakin da HKI ta shelanta akan Gaza a 2023.
Jirgin ruwan na “Madline” ya taso ne daga kasar Italiya, wata daya bayan da jirgin sama maras matuki na HKI ya kai hari akan wani jirin ruwan wanda ya nufi Gaza akan gabar ruwan Malta.
Daga cikin kayan da jirgin ruwan yake dauke da shi a kawai madarar jarirai, shinkafa, da kuma magunguna da injinan tace ruwa. Haka nan kuma yana dauke da gabobin jikin dan’adam na roba na yara, saboda a yi wa yaran Gaza da Isra’ila ta mayar masakai dashe.
Mafi yawancin masu fafutukar dake cikin jirgin sun fito ne daga kasashen turai, kamar Sweeden Jamus da Faransa. Sai kuma wasu daga Holland da Brazil.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Jirgin ruwan jirgin ruwan
এছাড়াও পড়ুন:
Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro
“Muna bincike wannan lamari, kuma muna tabbatar da cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka, za a kare shi. Ba za mu bari wani abu ya same shi (Yerima) ba matuƙar yana aikinsa yadda ya kamata kuma yana yin aikinsa sosai.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA