Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki
Published: 7th, June 2025 GMT
Shugaban ya ci gaba da cewa, idan har zamu rage nauyin aikin da ke a kan Tashar ta Lekki, wajen biyan kudade, ya kamata ima Tashar ta san da cewa, muna da bukatar kudade da dama, domin mu sawo kayayyaki da dama na gudanar da ayyuka a Tashar, musamman domin mu tabbatar da cewa, ma’aikatan mu, na ci gaba da gudnar da ayyuakansu, a Tashar, kamar yadda ake bukata.
Dantso ya kara da cewa, za a yi aiki da tsarin NSW na kasa, inda zai samar da kaso 95 a cikin dari na gudanar da ayyuka a Tashar, wanda ya jaddada cewa, hakan zai kara rubunya, kudaden shiga, ga Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
“Gudanar da hada-hadar kudade ta hanyar yin amfani da na’ura, zai kawar da biyan kadade ta hanyar yin amfani, da rasidan bayan kudade, a daukacin Tashohin Jiragen Ruwan kasar, “ A cewar Shugaban.
“Idan hakan ya wakana, muna da yakinin cewa, za mu kara samun kudaden samun kudaden shiga masu yawa, kuma ina tunanin, za mu duba yuwuar, rage kudin shigar na fiton Jiragen Ruwan, “ Inji Dantsoho.
Shugaban ya kuma yabawa mahukuntan na Tsahar ta Lekki, kan bayar da daukacin gudunmawar su, domin ganin an kara daga martabar Tashar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.
“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA