Rasha Ta Kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Kasar Ukraine Tare Da Janyo Mata Munanan Barna
Published: 7th, June 2025 GMT
Kasar Rasha ta kai wasu gagaruman hare-haren jiragen saman yaki marasa matuka ciki kan birnin Kharkiv na kasar Ukraine
Rasha ta kai wadannan gagaruman hare-haren ne ta hanyar amfani da jiragen saman marasa matuka ciki kan birnin Kharkiv na gabashin Ukraine. Magajin garin Kharkiv ya ce: Hare-haren da jiragen saman Rasha suka kai a tsakiyar birnin sun haddasa gobara da barna sosai.
Takaddama tsakanin Rasha da Ukraine na kara kamari a kasa duk da ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ke yi. Mjiyar sojin Ukraine ta amince cewa: Sojojin Rasha sun kaddamar da gagaruman hare-hare kan birnin Kharkiv da ke gabashin kasar Ukraine ne, lamarin da ya haifar da fashe-fashe a birnin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkatan wasu, da kuma barnata kayayyaki, da kona gine-gine da dama, a cewar magajin garin Kharkiv.
Rundunar sojin saman Ukraine ta ce: Rasha ta harba jiragen sama marasa matuka ciki da suka kai 200, da makamai masu linzami guda biyu, da kuma wasu nau’ukan makamai masu linzami guda shida cikin kasar.
Kafin wannan harin dai an kai harin ne da wani kazamin makami mai linzami da na Rasha da aka kai a kan birnin Kiev babban birnin kasar Ukraine, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkatan wasu.
Yayin da harin ya kawo cikas ga tsarin metro, a cewar mahukuntan kasar, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa: An kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da masu yawa a cikin jami’an tawagar bayar da agajin gaggawa a hare-haren da suka hada da makamai mai linzami da jirage masu saukar ungulu a babban birnin kasar da kuma arewa maso yammacin birnin Lutsk, inda ya yi kira da a matsa lamba kan Rasha.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Ukraine
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi
A ci gaba da yakin da suke yi da ’yan ta’adda, sojojin Najeriya sun samu nasarar jikkata jagoran kungiyar ISWAP, Abu Moussab Albarnawi a dajin Sambisa.
Bayanai sun nuna sojoji sun sami nasarar ce bayan wani gagarumin harin da suka kai ta sama a wani sabon sansani na ’yan ta’addan da ke dajin Baikee a yankin Sambisa a Jihar Borno.
Dakarun rundunar da ke karkashin Operation KALACHEN WUTA, wanda bangare ne na rundunar sojojin saman Najeriya da ke karkashin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ne suka kai harin.
Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Najeriya saboda yakin Isra’ila-Iran – Masana Majalisa ta aike wa Tinubu kudurorin dokar haraji domin ya rattaba musu hannuMajiyoyin sojojin Najeriya da ke rundunar OPHK wanda Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ke jagorantar ta ce an aiwatar da wannan aiki ne a dajin inda ’yan ta’addan suke ci gaba da taruwa a sabon sansanin da suka kafa tare da shirya kai hare-hare kan fararen hula da ke kusa, musamman garin Izge.
Majiyar ta ce wannan aikin da Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, Kwamandan Rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas a Operation Hadin ke jagoranta, da kuma kwamandan rundunar sojin sama, kwamanda UU Idris, suka shirya a ranar 13 ga watan Yuni 2025 a jere, yadda aka kai hare-hare da dama kan wuraren taruwar ’yan ta’addan, tare da lalata wasu manyan kadarori da kuma kashe manyan kwamandodi na kungiyar ta ISWAP
Kididdigar barnar da majiyoyi suka tabbatar an yi a harin ta tabbatar da cewa kungiyar ta yi mummunar asara.
Wasu majiyoyin leken asiri sun kara tabbatar da cewa fitaccen shugaban kungiyar ISWAP, Abu Moussab Albarnawi, ya samu munanan raunuka a fuskarsa yayin harin ta sama, duk da cewar har yanzu ba a tabbatar da matsayin raunin da ya ji ba.
Nasarar kawar da ’yan ta’addan da kuma wargaza yunkurinsu na sake haduwa ya rage musu karfin fada sannan ya jefa su cikin rudani.