‘Yansanda Sun Hallaka Ɗan Fashi Da Makami Tare Da Jikkata Wasu Da Dama A Bauchi
Published: 6th, June 2025 GMT
A cewarsa, jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa da ke cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun rufe babbar hanyar, sun fara yin fashi ga matafiya a ranar 4 ga watan Yunin 2025.
Nan take aka tura tawaga a ƙarƙashin jagorancin babban jami’in ɗansanda (DPO) da ke kula da caji ofis ɗin Toro, tare da haɗin guiwar sauran jami’an tsaro inda suka nufi wurin da nufin daƙile fashin.
Da isarsu wurin, suka fara musayar wuta inda jami’an tsaron suka samu nasarar fatattakarsu wanda hakan ya janyo da dama daga cikin ‘yan fashin suka gamu da raunuka na harbin bindiga sannan an harbe daya ya mutu nan take.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, an miƙa gawar Shagari ga sashin da ke kula da gawarwaki domin birne shi kamar yadda aka tanada.
Wakil ya ƙara da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin ganin an bi sawun sauran waɗanda ake zargin ‘yan fashi da makamin ne da suka tsere domin tabbatar da an kamo su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Soke Faretin Ranar Dimokuraɗiyya, Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan Ƙasa Jawabi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp